Labaran Duniya
Rikici na sake barkewa a gabas ta tsakiya yayin da Isra'ila ta kai hari kasar Lebanon inda ta kashe kwamandan Hisbullah, Fuad Shukr bayan kisan Isma'il Haniyeh.
Wanda ya kafa kuma dandanlin sada zumunta na Telegram, Pavel Durov, ya ba da labarin yadda ya haifi ‘ya’ya 100 a sassan duniya duk da cewa bai yi aure ba.
Sunan tauraron mawakin Afrobeats, Wizkid ya sake bazuwa a yanar gizo bayan da wani bidiyo na katafaren gidansa da ke Landan ya bazu. Mutane sun yi tsokaci.
A ranar Asabar ne hukumar ITA ta sanar da cewa, an dakatar da 'yar wasan damben nan ta Najeriya Cynthia Temitayo Ogunsemilore daga gasar Olympics ta birnin Paris.
Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya samu gayyata daga shugaban kasar Gabon, Brice Oligui Nguema domin ya zuba jari a harkar siminti da taki.
Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja daga birnin Accra na kasar Ghana, bayan halartar taron koli na tsakiyar shekara karo na 6 na kungiyar Tarayyar Afirka.
An saka 'yar wasan Super Falcons, Asisat Oshoala, da tsohuwar ‘yar wasan Najeriya, Perpetual Nkwocha, cikin jerin ‘yan wasa 25 da suka fi fice a Afirka.
Shugaban Kenya William Ruto na shirin kafa wata karamar gwamnati bayan korar daukacin ministocinsa bayan shafe makwanni ana zanga-zangar adawa da shirinsa na haraji.
Gawar tsohon shugaban majalisar dattawa, Joseph Wayas, ta iso Najeriya bayan kimanin shekaru uku da rasuwarsa a wani asibitin Landan a cikin watan Nuwamban 2021.
Labaran Duniya
Samu kari