Nahiyar Turai Ta Shiga Wani Irin Yanayi, Zanga Zanga Ta Ɓarke a Ƙasashe da Yawa

Nahiyar Turai Ta Shiga Wani Irin Yanayi, Zanga Zanga Ta Ɓarke a Ƙasashe da Yawa

  • Zanga-zangar da ake yi a Faransa, Sifaniya da wasu ƙasashen Turai na ci gaba sakamakon tsadar rayuwa
  • A Faransa, an kama mutane sama da 2,400, yayin da 'yan sandan Portugal suka kama wasu mutane 55 a birnin Lisbon saboda zanga-zangar
  • 'Yan siyasar masu ra'ayin dama na amfani da rikicin wajen neman goyon bayan jama'a, gabanin zaɓen shugaban Faransa da za a gudanar a Afrilun 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Paris, France - Zanga-zanga na ci gaba a Faransa, Sifaniya da sauran sassan Nahiyar Turai.

Majiyoyi sun ce zanga-zangar na neman a ɗauki mataki kan tsadar rayuwa, ƙarancin albashi, ƙarancin ingancin ilimi da cin hanci da rashawa.

Zanga-zanga ta ɓarke a Nahiyar Turai
Matashi yana jifa a cikin masu zanga-zanga da ke neman kawo sauyi saboda tsadar rayuwa. Hoto: The Guardian.
Source: UGC

Daga Faransa zuwa Portugal, Albaniya da Italiya, ana ci gaba da fuskantar rikice-rikicen zamantakewa, cewar

Zanga-zanga ta barke a Turai

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Yadda Tinubu, Atiku da Peter Obi ke fafatawar neman nasara a jihohin Arewa 5

Zanga-zangar ta kasance tare da sace-sace, raunata mutane da arangama tsakanin 'yan sanda da masu tayar da hankali.

A Sifaniya da Portugal, masu zanga-zangar sun kafa sansanonin tantuna domin nuna rashin amincewa da tsadar gidaje, yayin da matasan Turai ke fuskantar rashin tabbas game da makomarsu.

Rikicin na faruwa ne a daidai lokacin da jam'iyyun masu tsattsauran ra'ayin dama ke samun karɓuwa a wajen jama'a tare da samun gagarumar nasara a zaɓe.

Haka kuma, Turai na fuskantar wani muhimmin lokaci dangane da tallafin da take bai wa Ukraine, yayin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ke ƙoƙarin kulla dangantaka da Shugaban Rasha, Vladimir Putin.

A Faransa, zanga-zangar na faruwa ne gabanin zaɓen shugaban ƙasar da aka tsara gudanarwa a watan Afrilun 2027.

'Yan siyasar masu ra'ayin dama na amfani da wannan rudani a matsayin damar cimma burinsu, cewar Premium Times.

An yi zanga-zanga a Faransa
Shugaba Emmnuel Macron na kasar Faransa. Hoto: Emmnuel Macron.
Source: Getty Images

Tasirin da zanga-zangar ke yi

Masana sun bayyana cewa haɗuwar zanga-zangar tituna mai tsanani, tashin farashin makamashi da raunin shugabancin masu ra'ayin tsakiya na samar da kyakkyawan yanayi ga kamfen ɗin siyasar masu adawa da tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi artabu da tsagerun 'yan bindiga, an ceto mata bayan zubar da jini

A farkon makon nan, Marine Le Pen, shugabar jam'iyyar National Rally mai tsattsauran ra'ayin dama, ta danganta sace-sace da lalata dukiyoyin da suka biyo bayan zanga-zangar da abin da ta kira “shekaru da dama na shige da fice” zuwa Faransa.

Ta gabatar da jam'iyyarta a matsayin wadda za ta iya dawo da zaman lafiya da doka, tare da bayyana cewa shugabancin Shugaba Emmanuel Macron ba shi da wata “sahihiyar ƙima ko iko” a yanzu.

A sakamakon zaɓen ra'ayin jama'a na baya-bayan nan, Le Pen na kan gaba sosai, kuma ana ganin tana da damar zama shugabar Faransa ta gaba.

A gefe guda kuma, hukumomin Faransa sun bayyana cewa sun kama mutane sama da 2,400 a faɗin ƙasar.

Ɗalibai sun yi zanga-zanga a Faransa

A baya, an ji cewa dubban dalibai sun gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na Faransa, inda rikici ya barke tsakaninsu da ’yan sandan kwantar da tarzoma.

Zanga-zangar ta haddasa katse karatu a makarantu sama da 700, yayin da aka kona shara tare da kai hare-hare kan jami’an tsaro da kadarorin makarantu.

Hukumomin Faransa sun ce an kama mutane 1,747 a ranar Juma’a, yayin da aka samu raunuka da barna a makarantu da dama a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.