Zaben jihohi
Shugaban hukumar tattara haraji ta Najeriya, FIRS, Zacch Adelabu Adedeji, ya musanta jita-jitar tsaya wa takarar gwamna a jihar Oyo a zaben 2027 mai zuwa.
INEC na shirin lalata katunan zaɓe da ba a riga da an karɓa ba, inda za ta maye gurbinsu da fasahar BVAS don sauƙaƙe tantance masu zaɓe da tabbatar da ingancin zaɓe
Gwamnatin jihar Bauchi ta nada sababbin shugabanni, ciki har da Sakataren gwamnati da babban sakataren gwamna Bala Mohammed, inda za a rantsar da su a yau.
Shugaba Tinubu da gwamnoni sun bukaci 'yan Najeriya da su rundumi soyayya, zaman lafiya, da hadin kai yayin bikin Kirsimeti. Diri ya nemi a taimaki marasa galihu.
Popoola Olukayode Joshua, tsohon dan takarar gwamna na NNPP a Oyo, na shirin komawa APC. Ganduje ya bukaci shiri tun wuri don tazarcen Tinubu da nasarar APC a 2027.
Kwanaki shida bayan shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya sha alwashin kwace jihar Rivers, an roke shi ya yi kokarin karbe ikon Oyo daga jam'iyyar PDP.
APC ta fara zage damtse kafin zaben 2027. Jam'iyyar ta rasa Adamawa a zaben 2023. Ankafa kwamitin mutum takwas domin daidaita 'yan jam'iyyar kafin zaben.
Tsohon ministan kwadago a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari, Chris Ngige, ya ce shugabannin kananan hukumomi sun fi wasu gwamnonin karbar cin hanci da rashawa.
Wata kungiyar matasa 'yan asalin Legas sun bukaci Seyi, dan Shugaba Bola Tinubu da ya cire tunanin zaman gwamnan jihar Legas a 2027 domin ba za su bari ba.
Zaben jihohi
Samu kari