Dan Majalisar Tarayya Ya Gabatar da Kudirin Kafa Sabbin Jihohi 3 a Kudu Maso Yamma

Dan Majalisar Tarayya Ya Gabatar da Kudirin Kafa Sabbin Jihohi 3 a Kudu Maso Yamma

  • Dan majalisar wakilan tarayya, Oluwole Oke daga jihar Osun ya gabatar da kudirin ƙirƙirar sabbin jihohi uku a Kudu maso Yamma
  • Jihohin kamar yadda Oke ya zayyana a daftarin da ya gabatar wa magatakardar majalisar sun hada da; Oke-Ogun, Ijebu, da Ife-Ijesa
  • Idan kudirin ya zama doka, Kudu maso Yamma za ta kasance mafi yawan jihohi a cikin yankuna shida na kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Oluwole Oke, dan majalisar wakilai, ya gabatar da kudirin kirkirar sabbin jihohi uku a shiyyar kudu maso yammacin kasar.

Oke, wanda ke wakiltar mazabar Obokun/Oriade na jihar Osun, shine shugaban kwamitin majalisar kan harkokin shari’a.

Kara karanta wannan

AFCON: Tinubu ya aika muhimmin sako ga Super Eagles bayan ta yi rashin nasara a wasan karshe

Majalisar tarayya za ta duba yiwuwar kirkirar sabbin jihohi uku a Kudu maso Yamma.
Majalisar tarayya za ta duba yiwuwar kirkirar sabbin jihohi uku a Kudu maso Yamma. Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Bayani game da jihohin da ake nema kafawa

Kudirin ya ba da shawarar gyara jadawalin farko, sashe na 1 na kundin tsarin mulkin kasar don samar da sabbin jihohi uku; jihar Oke-Ogun, Ijebu, da Ife-Ijesa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daftarin kudurin ya nuna cewa jihar Oke-Ogun, tare da Iseyin a matsayin babban birninta, za ta kunshi kananan hukumomi 12.

A cewar kudirin dokar kamar yadda The Cable ta tattaro, jihar Ijebu, idan aka kirkire ta, za ta kunshi kananan hukumomi tara ne da Ijebu Ode a matsayin babban birninta.

Abin da zai faru idan kudurin ya zama doka

Hakazalika jihar Ife Ijesa za ta kunshi kananan hukumomi 11, da Ile-Ife a matsayin babban birninta.

Ana sa ran za a fara yi wa kudirin dokar karatun farko, wanda aka gabatar wa magatakardar majalisar dauke da kwanan wata 6 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Talaka zai sake shiga kunci, farashin man jirgin sama ya karu, an kara kudin sufuri a Najeriya

Idan har kudirin ya tsallake dukkan karatu kuma ya zama doka, Kudu maso Yamma za ta kasance mafi yawan jihohi a cikin yankuna shida na kasar.

Yan bindiga sun kashe dan takarar majalisar tarayya

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun kashe wani dan takarar majalisar tarayya na jam'iyyar PDP a jihar Anambra.

Dan takarar mai suna Jude Oguejiofor ya gamu da ajalinsa ne bayan da 'yan bindigar suka yi garkuwa da shi da dan uwansa.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun saki dan uwan amma suka kashe Oguejiofor lamarin da ya ja mahaifinsa ya hadiyi zuciya ya mutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel