An Bankado Wani Shirin Ganduje Na Tilasta Gwamna Mai Ci Komawa APC Don Kwace Jihar, Bayanai Sun Fito

An Bankado Wani Shirin Ganduje Na Tilasta Gwamna Mai Ci Komawa APC Don Kwace Jihar, Bayanai Sun Fito

  • Da alamu jam’iyyar ta matsa hannu sai ta kwace ikon jihar Anambra da ke karkashin jam’iyyar APGA na tsawon lokaci
  • Wata majiya ta tabbatar da cewa jam’iyyar na neman tilasta Gwamna Charles Soludo komawa APC tare da tsayawa takara
  • Sai dai jam’iyyar APGA ta yi watsi da lamarin inda ta ce wannan kawai wani fata ne na jam’iyyar APC da ta ke yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra – Yayin da jam’iyyar APC ke neman kwace kujerar gwamnan Anambra, an bayyana yadda suka sake sabon salo.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jam’iyyar na neman tilasta Gwamna Charles Soludo don komawa APC tare da tsayawa takara.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa PDP illa yayin da babban jigo a jam'iyyar ya koma APC

Akwai alamun APC na son kwace ikon wata jiha karfi da yaji
Ana zargin APC ta na matsawa Gwamna Soludo dole ya dawo jam'iyyar. Hoto: Abdullahi Ganduje, Charles Soludo.
Asali: Facebook

Mene ake zargin APC a Anambra?

Jam’iyyar na yin hakan ne a kokarin ganin ta karbe ikon jihar da ke Kudu maso Gabas a karkashin jam’iyyar APGA.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan shugabannin APC a yankin sun kai ziyara fadar Obi na Onitsha, Igwe Alfred Nnaemeka Achebe, cewar Vanguard.

Yayin ziyarar shugabannin jam’iyyar sun roki taimakon ganin jam’iyyar APC ta karbe ikon jihar a zaben shekarar 2025.

Wani jigon APC a birnin Awka ya ce masu ruwa da tsakin jam’iyyar na yawan ganawa da Soludo don matsa masa ya koma APC.

Ya ce hakan zai fi musu sauki su yi amfani da gwamna mai ci don ya yi takara a zaben 2025 tare da yin nasara.

Martanin jam'iyyar APGA a Anambra

Ya kara da cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar a jihar da kuma matakin kasa su na neman yadda za su karbe ikon jihar shi ne burinsu.

Kara karanta wannan

Hankalin Ganduje ya fara kwanciya bayan samun gagarumin alkawari daga dattawan jam'iyyar

Jigon na APC ya ce idan har hakan bai faru ba to su na da wani shiri na biyu wanda za su yi amfani da shi, Anambra Magazine ta tattaro.

Da ya ke martani kan matsin lambar, sakataren watsa labaran jam’iyyar APGA, Mazi Ejimofor ya bayyana cewa babu gaskiya a maganar.

Ya ce Gwamna Soludo ba irin mutumin da za a matsa masa lamba ba ne don ya koma wata jam’iyya.

Ganduje ya tafka asara

Kun ji cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun sauya sheka a jihar Kano mahaifar Abdullahi Ganduja.

Ciyamomin kananan hukumomi akalla uku ne suka koma jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel