Kotu Ta Soke Karar Jam’iyyar Adawa da Ke Kalubalantar Zaben Gwamnan Jihar Arewa, Ta Bayyana Dalili

Kotu Ta Soke Karar Jam’iyyar Adawa da Ke Kalubalantar Zaben Gwamnan Jihar Arewa, Ta Bayyana Dalili

  • Yayin da aka fara sauraran shari’ar zaben gwamnan jihar Kogi, kotu ta soke karar jam’iyyar APP da ke kalubalantar zaben
  • Kotun da ke zamanta a Abuja ta soke karar ce da ke neman tsige Gwamna Usman Ododo na jam’iyyar APC a jihar Kogi
  • A cikin wata takarda da ke neman janye karar da APP ta shigar, lauyan Gwamna Ododo, Ibrahim Mohammed ya amince da bukatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi – Kotun sauraran kararrakin zabe ta soke karar jam’iyyar APP da ke kalubalantar zaben jihar Kogi.

Kotun da ke zamanta a Abuja ta kori karar ce da ke neman tsige Gwamna Usman Ododo na jam’iyyar APC a jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta sake ba da sabon umarni ga likitoci kan 'yar Tiktok, Murja, ta fadi dalili

Kotu ta soke karar jam'iyyar adawa da ke kalubalantar gwamnan APC
Kotu ta soke karar jam'iyyar APP bayan ta nemi janye karar. Hoto: Usman Ododo.
Asali: Twitter

Wane mataki kotun ta dauka kan APP?

Alkalan kotun guda uku karkashin jagorancin Mai Shari’a, Ado Birnin-Kudu shi ya soke karar bayan lauyan jam’iyyar ya janye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar kan hukuncin da kotun ta dauka.

A cikin wata takarda da ke neman janye karar da APC ta shigar, lauyan Gwamna Ododo, Ibrahim Mohammed bai kalubalanci bukatar ba.

Har ila yau, lauyan jam’iyyar APC, DC Denwigwe shi ma ya bi sahu tare da lauyan hukumar INEC, Kanu Akanbi.

Kotun bayan duba dukkan korafe-korafen da bukatar janye karar daga lauyoyi da soke karar da jam’iyyar APP ke nema.

Yaushe jam'iyyar APP ta shigar da kara?

Yayin da kuwa kotun za ta ci gaba da sauraran korafe-korafe uku da ke gabanta wanda ke kalubalantar zaben.

Kara karanta wannan

Ana fama da tsadar rayuwa, annobar murar tsuntsaye ta fada wata jihar Arewa

Tun farko, jam’iyyar APP a ranar 1 ga watan Disambar 2023 ta shigar da kara don neman kifar da Gwamna Ododo a zaben da aka gudanar a watan Nuwamba.

Kamar yadda jam’iyyar ta tabbatar, ta janye karar ce saboda rashin hujjoji kan karar inda ta guji bata wa kotun lokaci.

An rantsar da Ododo a jihar Kogi

Kun ji cewa, An rantsar da Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi bayan ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin gwamna.

Rahotanni sun bayyana cewa dubunnan mutane ne suka halarci rantsar da sabon gwamnan a ranar 27 ga watan Janairun 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel