Yadda FAAC Ta Raba Wa FG, Jihohi da Ƙananan Hukumomi Naira Tiriliyan 1.1 a Watan Janairu

Yadda FAAC Ta Raba Wa FG, Jihohi da Ƙananan Hukumomi Naira Tiriliyan 1.1 a Watan Janairu

  • Asusun kasafin kudin Najeriya (FAAC) ya raba wa gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi naira tiriliyan 1.149 a watan Janairu
  • An samu wadannan kudaden ne daga harajin da gwamnatin ta tattara a watan Janairu, kama daga na VAT, EMT, SR, CIT, PPT da sauran su
  • Legit Hausa ta yi bayani dalla dalla kan adadin kudin da gwamnatin tarayyar, jihohi da kananan hukumomi suka samu a watan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Asusun kasafin kudin Najeriya (FAAC) ya raba wa gwamnatin tarayya, jihohi 36 da kananan hukumomin ƙasar naira tiriliyan 1.149 a watan Janairu.

An raba kudin ne a taron kwamitin asusun kasafin kudin na watan Fabrairu 2024 wanda ministan kudi kuma ministan kula da tattali, Wale Edun ya jagoranta.

Kara karanta wannan

Babban labari: EFCC ta cafke 'yan canji a Abuja, an gano dalili

FAAC ta raba wa FG, jihohi da kananan hukumomi naira tiriliyan 1.1 a watan janairu
FAAC ta raba wa FG, jihohi da kananan hukumomi naira tiriliyan 1.1 a watan janairu. Hoto: @NGRPresident@NGRPresident
Asali: Twitter

Yadda aka samu kudaden da aka kasafta

A cewar wata sanarwar bayan taro da FAAC ta fitar, kudin sun hada da naira biliyan 463 na harajin (DSR), da naira biliyan 391.7 na harajin (VAT), da harajin EMT na naira biliyan 15.9.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu harajin naira tiriliyan 2.068 a watan Janairu, wanda aka kashe naira biliyan 78.412 na karbar kudin, da kudin tallafi na naira biliyan 639.926 da suka hada da na ajiyar biliyan 200.

Gwamnati ta kuma karbi harajin (GSR) da ya kai naira tiriliyan 1.151 a watan Janairu 2024. Wannan ya zarce wanda ta karba a watan Disambar 2023 da tserayar naira biliyan 276.4.

Yadda aka kasafta wa gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi kudin:

Kudin da aka raba daga harajin doka

Daga kudaden harajin doka na naira biliyan 463.079 da aka raba:

Kara karanta wannan

Jerin jihohin Najeriya 10 da aka fi samun kayan abinci da tsada, Kogi na kan gaba

  • Gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 216.757
  • Gwamnonin jihohi sun karbi naira biliyan 109.942
  • Kananan hukumomi sun samu naira biliyan 84.761

An raba wa jihohi masu cin gajiyar kudaden shiga daga ma'adinai naira biliyan 51.619.

Kudin da aka raba daga harajin VAT

  • Gwamnatin tarayya ta karbi naira biliyan 58.768
  • Gwamnonin jihohin sun samu naira biliyan 195.894
  • Kananan hukumomi sun samu naira biliyan 137.125

Kudin da aka raba daga harajin EMTL

  • Gwamnatin tarayya ta karbi naira biliyan 2.388
  • Gwamnonin jihohi sun karbi naira biliyan 7.961
  • Kananan hukumomin sun samu naira biliyan 5.573

Kudin da aka raba daga harajin canjin kudi

  • Gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 129.354
  • Gwamnonin jihohin sun karbi naira biliyan 65.610
  • Kananan hukumomi sun samu naira biliyan 50.582

An raba wa jihohi masu cin gajiyar kudaden shiga daga ma'adinai naira biliyan 33.482.

Sanarwar ta ce harajin da aka samu a cikin watan Janairu 2024 daga harajin shigar kudin kamfanoni (CIT), harajin shigo da kaya, harajin ribar man fetur (PPT) da harajin mai da gas ya ƙaru sosai.

Kara karanta wannan

Kano da Kaduna sun shiga jerin jihohi 33 da 'yan kasashen waje suka ki zuba hannun jarinsu

Sai dai kuma sanarwar ta ce harajin kimar aiki (VAT), harajin fitar da kaya, harajin tura kudi ta banki (EMTL) da harajin CET sun ragu sosai.

Yanzu abin da ya yi saura a cikin asusun ECA shine dala 473,754.57.

Asali: Legit.ng

Online view pixel