Bayan Rasa Wasu Jiga-jigai a Kano, APC Ta Samu Karuwa Bayan Jigon PDP Ya Koma Jam'iyyar

Bayan Rasa Wasu Jiga-jigai a Kano, APC Ta Samu Karuwa Bayan Jigon PDP Ya Koma Jam'iyyar

  • Jam’iyyar PDP ta tafka asara bayan jigon jam’iyyar a jihar Ondo ya watsar da jam’iyyar tare da komawa jam’iyyar APC
  • Dan siyasar mai suna Hon. Tomide Akinribido tsohon dan Majalisar jihar ce da ya wakilci mazabar Ondo ta Yamma a jihar
  • Akinribido ya sanar da haka ne a cikin wata sanarwa a jiya Juma’a 9 ga watan Faburairu a karamar hukumar Ondo ta Yamma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo – Tsohon mamban Majalisar jihar Ondo, Hon. Tomide Akinribido ya watsar da kashin jam’iyyar PDP.

Akinribido ya sanar da haka ne a cikin wata sanarwa a jiya Juma’a 9 ga watan Faburairu a karamar hukumar Ondo ta Yamma.

Kara karanta wannan

Bayan lashe zaɓe, ƴan majalisa sun zaɓi sabon shugaban majalisar dokoki a jihar Arewa

Jigon jam'iyyar PDP ya sauya sheka zuwa APC
Hon. Tomide ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC daga PDP. Hoto: Abdullahi Ganduje, Umar Damagun.
Asali: Facebook

Jigon PDP ya sauya sheka zuwa APC

Tsohon dan Majlisar ya kuma sanar da sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulkin jihar, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce zai yi rijista a matsayin mamban jam’iyyar APC mai mulkin jihar a ranar Litinin 12 ga watan Faburairu.

Wannan na zuwa ne watanni kadan kafin gudanar da zaben gwamnan jihar a karshen wannan shekara da muka ciki.

An fara zaban Tomide ne a matsayin dan Majalisar jihar a shekarar 2019 don wakiltar Ondo ta Yamma 1 a karkashin jam’iyyar ZLP.

Yadda Akinribido ya sha kaye a zabe

Dan siyasar ya sauya sheka daga jam’iyyar ZLP zuwa jam’iyyar PDP mai adawa a kasar daf da zaben shekarar 2023, cewar Tribune.

Akinribido ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2023 a jam’iyyar PDP inda ya sha kaye a hannun matashi dan shekaru 33.

Kara karanta wannan

Akpanudoedehe: Dan takarar gwamnan NNPP ya lissafa sharuddan komawa APC

Matshin mai suna Otunba Moyinolorun Ogunwumiju ya yi takara a jam’iyyar APC a zaben da aka gudanar a watan Maris din shekarar 2023.

Ciyamomi 3 sun watsar da APC a Kano

Kun ji cewa jam’iyyar APC a jihar Kano ta tafka babbar asara bayan rasa ciyamomin jam’iyyarta har guda uku.

Ciamomin sun hada da na kananan hukumomin Dawakin Tofa da Garun-Malam sai kuma karamar hukumar Nassarawa da ke jihar.

Wannan na zuwa ne makwanni biyu bayan shugaban jam’iyyar APC, Umar Ganduje ya roki ‘yan jam’iyyar NNPP su dawo APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel