An Yamutsa APC, Ganduje, An Tsaida ‘Yan Takara 3 Masu Neman Kujerar Gwamna 1

An Yamutsa APC, Ganduje, An Tsaida ‘Yan Takara 3 Masu Neman Kujerar Gwamna 1

  • Bangarori dabam-dabam sun shirya zabukan tsaida gwani na APC, kowanensu ya fito da ‘dan takaransa na zaben Gwamnan jihar Edo
  • Kwamitin da APC-NWC ta aika zuwa Edo ta ce Dennis Idahosa ne ‘dan takara, amma ‘dan majalisar ya samu kishiyoyi a jam’iyya
  • Tsagin Osagie Ize-Iyamu sun tsaida Sanata Monday Okpebholo sai kuma aka samu wadanda suka ba Anamero Dekeri tikitin APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A halin da ake ciki a yanzu, an bar kan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a rarrabe bayan shirya zabukan tsaida gwani a jihar Edo.

Rikicin da aka samu kamar yadda Daily Trust ta rahoto shi ne mutane akalla uku su ke ikirarin su za su rikewa APC tuta a Edo.

Kara karanta wannan

‘Dan siyasa ya hakura da kujera, saboda magudi aka shirya domin ya lashe zaben majalisa

Edo APC
'Yan takaran APC a Edo Hoto: @Hope_Uzodimma1, @OfficialAPCNig
Asali: Twitter

Edo 2024: Jam'iyyar APC ta tsaida Idahosa

Da farko Hon. Dennis Idahosa shi ne wanda aka rahoto cewa kwamitin Gwamna Hope Uzodimma ya sanar a matsayin ‘dan takara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Dennis Idahosa ‘dan majalisa ne mai-ci wanda yake wakiltar mazabar Ovia.

...wasu sun ba Okpebholo takara a APC

Ba a dade ba sai aka ji labarin tsaida Sanata Monday Okpebholo a zaben da aka gudanar a gidan tsohon 'dan takara, Osagie Ize-Iyamu.

Dr. Stanley Ugboaja ya ce Sanatan shi ne wanda ya lashe zaben tsaida gwanin jam’iyyar.

...ko Anamero Dekeri zai rike tutar APC

Jaridar ta ce ana haka kuma sai aka ji wasu shugabannin APC daga kananan hukumomi sun tsaida wani ‘dan takaran dabam.

Ojo Babatunde ya sanar da sakamakon zaben tsaida ‘dan takara da suka gudanar, yake cewa Anamero Sunday Dekeri ya yi galaba.

Kara karanta wannan

Rikici ya shigowa ‘yan APC, an aikawa Shugaban kasa korafin sabon Gwamna

Wanene 'dan takaran asali a APC?

Wata kungiyar ‘yan APC a karkashin jagorancin Emmanuel Godwin ta ce babu yadda kwamitin Uzodinma zai yi da su Ojo Babatunde.

Amma kakakin APC na kasa, Felix Morka ya fitar da jawabi a ranar Lahadi, ya tabbatar da kwamitin Uzodinma kadai aka sani.

APC ba ta san da zaman kowa ba sai Uzodinma

Gwamnan Imo kuma shugaban gwamnonin APC shi ne shugaban kwamitin da jam'iyyar APC ta kafa ya gudanar da zaɓen gwani.

An ji za ayi zaben sabon gwamnan jihar Edo a watan Satumba mai zuwa, jam’iyyar APC ta tsaida wanda shi zai zama ‘dan takaranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel