APC Ta Sanar da Dan Takararta Na Gwamna a Zaben Fidda Gwani da Aka Gudanar, Bayanai Sun Fito

APC Ta Sanar da Dan Takararta Na Gwamna a Zaben Fidda Gwani da Aka Gudanar, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da ake shirye-shiryen zaben jihar Edo, Dennis Idahosa ya yi nasarar zama dan takarar gwamna a APC
  • A yau Asabar ce 17 ga watan Faburairu aka gudanar da zaben fidda gwani a zaben da za a gudanar a watan Satumba
  • Dan Majalisar Tarayya, Dennis Idahosa shi ya yi nasarar kasancewa dan takarar gwamnan a jam'iyyar APC a jihar Edo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Dan Majalisar Tarayya, Dennis Idahosa ya samu nasarar kasancewa dan takarar gwamnan APC a jihar Edo.

Dennis ya fito neman takarar gwamnan ne a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, cewar Channels TV.

APC ta sanar da dan takararta a zaben gwamnan jihar Edo
Dennis Idahosa ya yi nasarar kasancewa dan takarar APC a jihar Edo. Hoto: Dennis Idahosa.
Asali: Facebook

Yaushe aka gudanar da zaben fidda gwani?

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamna a APC ya sake janye takara ana daf da zabe, ya fadawa Ganduje dalilansa

A yau Asabar ce 17 ga watan Faburairu aka gudanar da zaben fidda gwanin jam'iyyar don tsayar da dan takarar a zaben watan Satumba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma shi ya jagoranci gudanar da zaben fidda gwanin da aka gudanar a yau Asabar 17 ga watan Faburairu.

Kwamitin da Uzodinma ke jagoranta shi ya sanar da Idahosa a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin, cewar Vanguard.

Yadda sakamoakon zaben ya kasance a Edo

Uzodinma ya ce Idahosa ya samu kuri'u dubu 40 inda ya doke sauran 'yan takara da ke neman kujerar.

Wannan nasara ta Idhosa ya tabbatar da shi a matsayin wanda zai tsaya takara a zaben da za a gudanar a watan Satumba.

Bayan samun nasara a zaben fidda gwanin, Idahosa ya yi godiya ga ubangiji da kuma sauran 'yan jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bayyana wanda APC zata baiwa tikitin takarar gwamnan jihar Edo a 2024

Idahosa shi ne ke wakiltar mazabar Ovia a Majalisar Tarayyar Najeriya kafin tsayawa neman wannan takara.

Dan takarar APC ya janye daga takara

Kun ji cewa dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo, Fasto Ize-Iyamu ya janye daga takarar gwamnan a zaben da za a yi.

Ize-Iyamu ya janye takarar ce ana saura kwana daya zaben fidda gwanin da aka gudanar a yau Asabar 17 ga watan Faburairu.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 21 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel