Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Daba Suka Hargitsa Zaben Cike Gurbi da INEC Ke Gudanarwa a Jihar Enugu

Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Daba Suka Hargitsa Zaben Cike Gurbi da INEC Ke Gudanarwa a Jihar Enugu

  • Wasu 'yan daba sun kai farmaki wuraren da ake gudanar da zaben cike gurbi a mazabar Enugu ta Gabas da ke jihar Enugu
  • Hukumar INEC ce ta sanar da hakan a shafinta na X a ranar Laraba, inda ta ce 'yan dabar sun lalata kayayyakin zaben gaba daya
  • A hannu daya kuma INEC ta ce tana ci gaba da gudanar da zabe a kananan hukumomi uku na jihar Taraba, kuma zaben na tafiya dai dai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Enugu - Hukumar zabe ta ƙasa INEC ta ce wasu 'yan daba sun hargiza zaben cike gurbi da jami'an hukumar ke gudanarwa a jihar Enugu.

Idan ba a manta ba, kotu ce ta ba INEC umurnin gudanar da zaben cike gurbi a mazabar Enugu ta Kudu a majalisar jihar.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sanda suka kama masu laifi 400 a jihar APC

INEC ta wallafa bidiyon yadda aka lalata kayayyakin zabe a jihar Enugu.
INEC ta wallafa bidiyon yadda aka lalata kayayyakin zabe a jihar Enugu. Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

INEC ta fitar da sanarwar farmakar jami'anta a Enugu

Hukumar a shafinta na X a ranar Laraba ta ce 'yan dabar sun lalata dukkanin kayayyakin zabe amma babu wanda aka ji wa rauni daga farmakin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta ce:

"Ofishin hukumar mu na jihar Enugu ya sanar da mu cewa wasu 'yan daba sun hargitsa zaben da ake yi a mazabar Enugu ta Gabas.
"Tuni jami'an mu suka bar wajen ta hanyar samun taimako daga jami'an tsaro."

Zaben cike gurbi a jihar Taraba na gudana cikin kwanciyar hankali

INEC ta kuma shaida cewa zaben da take gudanarwa a mazabar Jalingo/Yorro/Zing na majalisar jihar Taraba na gudana cikin kwanciyar hankali.

INEC na gudanar da zaben a kananan hukumomi ukun ne domin cike gurbin kujerar dan majalisar tarayyar su kamar yadda kotu ta bukata.

Kara karanta wannan

Hisbah ta Kano ta kwace kwalaben giya 8,600, ta kama 15 kan karuwanci

Duba sanarwar da INEC ta fitar a kasa:

An rantsar da Diri matsayin gwamnan Bayelsa karo na biyu

A wani labarin na yau Laraba, Legit Hausa ta ruwaito cewa Douye Diri, ya yi rantsuwar kama aiki matsayin gwamnan jihar Bayelsa a wa'adi na biyu.

Da misalin karfe 1:58 na rana, babban mai shari'a na jihar ya karanta wa Diri rantsuwar kama aikin a babban filin wasanni na Samson Siasia da ke babban birnin jihar, Yenagoa.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan na daga cikin wadanda suka halarci taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.