Labaran garkuwa da mutane
Wasu mutane ɗauke da makamai sun farmaki motar bus dake ɗauke da ɗaliban makarantar kwalejin sojojin ruwa, inda suka yi awon gaba da su baki ɗaya a jihar Edo.
Yayin da jihar Kaduna ke kara faɗawa cikin ƙalubalen sace-sacen mutane musamman sarakuna, wasu da ba'asan ku su waye ba sun yi awon gaba da wani basaraken Jaba.
Bayan sakin 28 daga cikin dalibai 121 da suka sace a makarantar Bethel Baptist Kaduna, yan bindigan sun bayyana tsarin da zasu bi wajen sakin ragowar daliban.
Wasu mutane ɗauke da makamai sun tare wasu manyan hanyoyi biyu a jihar Sokoto ranar Lahadi, inda suka sheke mutum biyu, sannan suka tafi da kusan mutane 100.
Rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna ta sanar da nasarar kubutar da dalibai biyu daga cikin daliban makarantar Bethel Baptist da aka sace a jihar Kaduna.
Wasu yan bindiga da ba'asan ko su waye sun kutsa kai cikin asibiti, inda suka yi awon wani kwararren likita, Solomon Nidiamaka, dake aiki a wurin ranar Litinin.
Wasu mutane dauke da makamai da ake zargin fulani.makiyaya ne sun hallaka mutane akalla goma a yankuna karamar hukumar Guma dake jihar Benuwai ranar Lahadi.
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana munin halin da Najeriya ke ciki, inda yace bindiga da harsasai ba za su iya magance matsalolin da ake ciki ba.
Bayan kwanaki biyar a hannun masu garkuwa da mutane, sarki mai daraja ta farko a jihar Kogi ya samu kuɓuta daga hannun waɗanda duka yi garkuwa da shi jiya.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari