Mai fada a ji ga Buhari: Ka san yadda zaka yi Jonathan ya gaje ka a zaben 2023

Mai fada a ji ga Buhari: Ka san yadda zaka yi Jonathan ya gaje ka a zaben 2023

  • Gabanin zaben 2023, ana ta yada jita-jitar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana zawarcin magabacinsa Dr. Goodluck Jonathan a asirce zuwa jam'iyyar APC mai mulki
  • A wani yanayi na daban, wani tsohon mai fada a ji ya bukaci shugaban kasar da ya yi wa Jonathan kamfe a zabe mai zuwa, ganin cewa shi ne zabin mutane
  • A halin da ake ciki dai har yanzu Jonathan bai yi magana game da rade-radin da ake yi na alaka da jam’iyyar APC ba

Josiah Oyakonghan (da aka fi sani da Oyimi) ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya mikawa Goodluck Jonathan shugaban kasa a 2023 kasancewarsa dan yankin Kudu.

Oyimi dai shi ne tsohon jagoran rusasshiyar kungiyar Movement for the Emancipation of Niger Delta (MEND), kuma shugaban kungiyar Movement for the Actualization of the Dreams of Niger Deltans (MADND).

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

Jigon mai fada a ji ya yi wannan roko ne yayin ganawa da manema labarai, inda ya bayyana cewa, Goodluck Jonathan ne kawai ‘yan Najeriya za su iya amincewa ya warware musu dimbin matsalolin da ke damunsu, in ji rahoton Vanguard.

Ana kira Jonathan ya dawo ya gaji Buhari
Ka san yadda zaka yi Jonathan ya dawo mulki a 2023, jigon siyasa ga Buhari | Hoto: vamguardngr.com
Asali: UGC

Yace:

“Da farko, muna taya daukacin ‘yan Najeriya murna a wannan bikin Easter, musamman ga Shugaba Buhari.
"Don haka muna amfani da wannan bukin na Easter domin jan hankalin ‘yan Najeriya da su ci gaba da marawa gwamnatin shugaba Buhari baya domin ganin ya cika alkawarin kawo sauyi da muka kagu da gani, sannan kuma ya yi wa Jonathan aiki ya dawo Villa.”

Kari a bayansa, ya kuma lura cewa duba da irin kalubalen da ke damun al’umma, mafita a hannun Jonathan take.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda Ganduje ya kalli Wike ido cikin ido ya fada masa cewa ba zai kai labari ba a 2023

Josiah Oyakonghan ya bukaci shugaba Buhari da ya yi wa Jonathan kamfen t=a yadda zai kubutar da al’ummar kasar tare da farfado fatan hadin kan kasa da ci gabanta.

Daily Post ta naqalto Josiah na cewa:

“Goodluck Jonathan mutum ne mai hazaka da gogewa, kuma a halin yanzu kasar nan na bukatar sa kuma mun yi sa’ar samun sa. Bayan sa'a sai kuma aiki.
"Don haka ya kamata shugaba Buhari ya goyi bayan GEJ ya shugabanci kasar don ganin an samu daidaituwar lamura a kasarmu. Kusan kowane bangare na rayuwarmu na bukatar kulawar gaggawa kuma GEJ shine mafita."

Ko matarsa bata yarda da tafiyar mulkinsa ba: Fasto Kukah ya sake caccakar Buhari

A wani labarin, babban limamin cocin nan da ke tasa Buhari a gaba, Matthew Kukah, ya ce Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ita ma ta amince da abin da ya fada game da mijinta.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Yanzu dai 'yan Najeriya sun fahimci PDP ce gatansu, in ji Sule Lamido

Kukah ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a safiyar ranar Talata, kamar yadda jaridar Punch ta tattaro.

Bishop din yayin da yake karin haske ya bayyana cewa babu wani abu tsakaninsa da Shugaban kasa Buhari illa dai kawai manufofinsa da ko da kuwa matarsa Aisha ma ta ki aminta da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel