Sabon hari: ‘Yan bindiga sun budewa jama'a wuta, sun hallaka wani adadi mai yawa

Sabon hari: ‘Yan bindiga sun budewa jama'a wuta, sun hallaka wani adadi mai yawa

  • Rahoton da muke samu daga majiya ya bayyana cewa, wasu 'yan bindiga sun farmaki jihar Imo jiya Lahadi
  • Wannan harin ya biyo bayan kisan gilla da aka yiwa wani jami'in hukumar zabe mai zaman kanta (INEC)
  • Ya zuwa yanzu dai ba a samu jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar ba, amma an ce mutane da dama sun jikkata

Jihar Imo - Rahoto ya bayyana cewa an kashe wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Orlu ta jihar Imo.

TheCable ta ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun kai farmaki karamar hukumar ne a ranar Lahadi da yamma, inda suka bude wuta kan fararen hula kafin jami’an tsaro su yi kicibis da su.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun tsare mai tsohon ciki, ta na kokarin nakuda, su na neman kudin fansa

An ce mutane da dama sun jikkata a harin, wanda kuma ya yi sanadiyar lalata gine-gine a yankin.

Yadda 'yan bindiga suka barnata abubuwa da dama a jihar Imo
Sabon hari: ‘Yan bindiga sun budewa jama'a wuta, sun hallaka wani adadi mai yawa | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Mike Abattem, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Imo, har yanzu bai amsa kiran da aka yi masa don tabbatar da faruwar harin ba.

Wani rahoton da jaridar Vanguard ta fitar ya ce, jami'an tsaro da 'yan bindiga sun yi artabu a yankin.

A ‘yan watannin nan dai jihar ta sha fama da hare-hare da dama daga ‘yan bindigar da ba a san ko su waye ba.

Lamarin dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da aka harbi wani jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a karamar hukumar Ihitte Uboma da ke jihar.

Wasu jami’an INEC guda biyu ne aka bayyana bacewarsu a harin wanda ya faru a ranar Alhamis din da ta gabata. Amma daga baya aka same su.

Kara karanta wannan

Sabon tashin hankali ya kunno kai a Sweden yayin da wasu ke shirin kone Al-Qur'ani

Sakamakon wannan lamari ne hukumar ta INEC ta dakatar da ci gaba da gudanar da rijistar masu kada kuri’a a karamar hukumar.

Zamfara: Dan bindiga Nasanda ya ba Matawalle kwana 14 ya biya shi N30m, ko ya halaka rayuka 300

A wani labarin, Nasanda, wani shahararren mai garkuwa da mutane a jihar Zamfara ya bai gwamnatin jihar wa'adin kwana 14 da ta biya shi N30 miliyan a matsayin diyyar matarsa da 'yan uwanta biyu.

Ya yi barazanar kashe rayuka 300 idan har ba a cika masa bukatarsa ba, Vanguard ta ruwaito.

Nasanda ya yi ikirarin cewa amaryarsa, kawunta da innarta duk 'yan sa kai ne suka halaka su a jihar. HumAngle ta ruwaito cewa, a wani sautin murya da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani, Nasanda ya ce da gangan aka kashe masa amaryarsa, kawunta da innarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel