Martanin fadar Buhari ga Fasto Kukah: Masu baki irin naka ne suka hargitsa kasar nan

Martanin fadar Buhari ga Fasto Kukah: Masu baki irin naka ne suka hargitsa kasar nan

  • Bai kamata a zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da haddasa rabuwar kai a Najeriya ba a cewar Femi Adesina
  • A sakamakon haka ne Femi; mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya zargi masu sukar shugaban da raba kan 'yan kasa
  • A cewarsa, wadanda suka raba kasar da bakunansu, da munanan maganganu sakaka, su ne suka haddasa rabuwar kai

Aso Rock Villa, Abuja - Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya wanke mai gidansa, shugaban kasa Muhammadu Buhari daga sukar da ake masa na cewa salon mulkinsa ya raba kan 'yan Najeriya.

Wani Babban Limamin Katolika na Diocese da ke Sokoto, Matthew Kukah, a ranar Lahadi, ya yi kakkausar suka ga Buhari kan rashin tsaro, cin hanci da rashawa, da rarrabuwar kawuna a Najeriya.

Kara karanta wannan

Limaman cocin Katolika da Anglika sun bukaci Buhari da yayi murabus

Martanin na kusa da Buhari ga Fasto Kukah
Martanin fadar Buhari ga Fasto Kukah: Masu baki irin naka ne suka hargiza kasar nan | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Kukah ya bayyana kokensa a cikin sakonsa na Ista mai taken, ‘To mend a broken nation: The Easter metaphor’.

A cewar Bishop din, 'yan siyasa sun lalata kowane fanni na rayuwa a Najeriya yayin da suke cin hanci da rashawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai a martanin da ya mayar kan batun Kukah, mai magana da yawun shugaban kasar ya ce abin mamaki ne a ce wadanda suke da laifin haifar da rarrabuwar kawuna a Najeriya su ne ke zargin shugaban kasar da irin laifin da suka aikata.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter Adesina ya rubuta cewa:

“Wadanda suka raba Najeriya da bakunansu, da muggan maganganu, magana babu birki, su ne wai yanzu suke tuhumar Shugaba Buhari. Abin bakin ciki! Mugun nufinsu ba zai cika ba.”

Shirin 2023: Yanzu dai 'yan Najeriya sun fahimci PDP ce gatansu, in ji Sule Lamido

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya fadawa masu neman kujerar shi a APC da su ka hadu a fadar Aso Villa

A wani labarin, Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa, ya ce a yanzu da 'yan Najeriya na kallon jam'iyyar PDP a matsayin fata daya tilo a garesu, TheCable ta tattaro.

Da yake magana yayin wani shiri a gidan Talabijin na Channels, a ranar Lahadi, tsohon gwamnan ya ce shirye-shiryen da jam’iyyar ke ci gaba da yi dangane da babban zaben 2023 na ganin amfani da ci gaban kasa ne.

Ya ce neman goyon baya da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP ke yi a fadin kasar nan zai kara daukaka martabar jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel