Ko matarsa bata yarda da tafiyar mulkinsa ba: Fasto Kukah ya sake caccakar Buhari

Ko matarsa bata yarda da tafiyar mulkinsa ba: Fasto Kukah ya sake caccakar Buhari

  • Faston nan da ya yi kaurin suna wajen caccakar Buhari ya sake yin jawabi, ya ce ko Aisha Buhari ba ta goyon bayan Buhari
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci ga fadar shugaban kasa kan martanin da ta yi na jawabansa na baya
  • A baya ya caccaki shugaba Buhari, inda yace mulkin Buhari ya raba kan 'yan Najeriya da dama a shekarun nan

Babban limamin cocin nan da ke tasa Buhari a gaba, Matthew Kukah, ya ce Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ita ma ta amince da abin da ya fada game da mijinta.

Kukah ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a safiyar ranar Talata, kamar yadda jaridar Punch ta tattaro.

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Har Yanzu FG Ba Ta Tura Wa Ƴan Bindiga Jiragen Yaƙin Tucano Su Ragargaje Su Ba, Fadar Shugaban Ƙasa

Sabon bayanin fasto Kukah kan shugabancin Buhari
Ko matarsa bata yarda da tsarukansa ba: Fasto Kukah ya sake caccakar Buhari | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bishop din yayin da yake karin haske ya bayyana cewa babu wani abu tsakaninsa da Shugaban kasa Buhari illa dai kawai manufofinsa da ko da kuwa matarsa Aisha ma ta ki aminta da su.

Kukah ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Duk masu cewa na soki shugaban kasa, ban taba sukar halinsa ba. Duk abin da na yi magana a kai shi ne rashin iya tafiyar da al’amuransa daban-daban yadda ya kamata kuma daidai. Na karanci bambance-bambance a matsayin darasi don haka na san abin da nake magana akai."

Ya bayyana cewa, ya yi imani da cewa Buhari mutumin kirki ne, amma dai ba shugaba ne nagari ba idan aka duba yadda yake mulki.

A cewarsa, yana matukar mutunta shugaban kasa da kuma halayensa da ya ce Buhari mutumin kirki ne amma idan ya kalle shi a matsayin shugaban kasa, to gaskiya ya gaza wajen gudanar da aikinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari tayi magana a kan ceto Bayin Allah da aka sace a jirgin Kaduna-Abuja

Kukah wanda ya tabbatar da cewa yana magana kai tsaye da shugaban kasar ya ce sukar da yake yiwa gwamnati ba wani abu bane na kashin kai illa kishin ganin al'amura sun daidaita a kasar.

Martanin fadar Buhari ga Fasto Kukah: Masu baki irin naka ne suka hargitsa kasar nan

Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya wanke mai gidansa, shugaban kasa Muhammadu Buhari daga sukar da ake masa na cewa salon mulkinsa ya raba kan 'yan Najeriya.

Wani Babban Limamin Katolika na Diocese da ke Sokoto, Matthew Kukah, a ranar Lahadi, ya yi kakkausar suka ga Buhari kan rashin tsaro, cin hanci da rashawa, da rarrabuwar kawuna a Najeriya.

Kukah ya bayyana kokensa a cikin sakonsa na Ista mai taken, ‘To mend a broken nation: The Easter metaphor’.

A cewar Bishop din, 'yan siyasa sun lalata kowane fanni na rayuwa a Najeriya yayin da suke cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Martanin fadar Buhari ga Fasto Kukah: Masu baki irin naka ne suka hargitsa kasar nan

Shirin 2023: Yanzu dai 'yan Najeriya sun fahimci PDP ce gatansu, in ji Sule Lamido

A wani labarin, Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa, ya ce a yanzu da 'yan Najeriya na kallon jam'iyyar PDP a matsayin fata daya tilo a garesu, TheCable ta tattaro.

Da yake magana yayin wani shiri a gidan Talabijin na Channels, a ranar Lahadi, tsohon gwamnan ya ce shirye-shiryen da jam’iyyar ke ci gaba da yi dangane da babban zaben 2023 na ganin amfani da ci gaban kasa ne.

Ya ce neman goyon baya da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP ke yi a fadin kasar nan zai kara daukaka martabar jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel