Iftala'i: Bam ya tashi a Taraba, mutane 3 sun mutu, wasu da dama sun jikkata

Iftala'i: Bam ya tashi a Taraba, mutane 3 sun mutu, wasu da dama sun jikkata

  • Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, akalla mutane 20 ne suka jikkata yayin da wani bam ya tashi a gidan cin abinci
  • An ruwaito cewa, mutum uku sun mutu, yayain da aka kai wadanda suka jikkata cibiyar kula da maras lafiya
  • Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ne ta tabbatar da faruwar lamarin, inji rahotannin da muke samu

Ardo Kola, Taraba - Ana fargabar mutane da dama ne suka mutu sakamakon fashewar abm a garin Iware dake karamar hukumar Ardo Kola a jihar Taraba.

Majiyoyi sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa bam din ya tashi ne a wani gidan cin abinci da ke da yawan cunkoson jama’a.

Bam ya tashi a gidan cin abinci
Iftala'i: Wani abu ya fashe a Taraba, mutane sun mutu, wasu da dama sun jikkata | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sama da mutane 20 da suka hada da mata ne suka samu raunuka a lamarin. Rahotanni sun bayyana cewa an garzaya da su cibiyar kula da maras lafiya ta tarayya dake Jalingo.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya ce mutane uku sun mutu yayin da 19 suka samu raunuka.

Ya kara da cewa, wannan shi ne karo na biyu da irin wannan fashewar ta afku, inda na farko ya afku a wata makarantar Katolika da ke Mutum Biyu, hedikwatar karamar hukumar Gassol mai tazarar kilomita 30 da juna wata guda da ya gabata, inji rahoton Channels Tv.

Usman ya kara da cewa an shirya jami’an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru domin fara bincike tare da kawar da tashin hankalin da hakan ya haifar.

Yadda lamarin ya faru inji wani shaidan gani da ido

Wani shaidan gani da ido Sunday Pantuvo, wanda ya tsere da kyar da raunuka ya ce wanda ake zargin ya dasa bam din ya zo mashayar ne tare da abokinsa a matsayin kwastomomi, ya nemi a basu barasa kana suka fice ta hanyoyi daban-daban.

Kara karanta wannan

Ku kawo fansa ko mu kashe sauran: 'Yan bindiga sun hallaka mutum 3 da suka sace a Kaduna

Daga baya wanda ake zargi da tayar da bam din ya dawo, ya biya kudin barasar sannan ya jefar da wata jakar leda wadda aka ce tana dauke da bam din sannan ya koma gefe.

Bayan 'yan mintoci kadan, ya ce zai tafi duba abokinsa, jim kadan aka ji tashin bam.

Pantuvo ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin ya tayar da bam din ne daga baya fusatattun mazauna garin suka kama shi suka kashe shi inda suka yi gunduwa-gunduwa da gawarsa.

Ku kawo fansa ko mu kashe sauran: 'Yan bindiga sun hallaka mutum 3 da suka sace a Kaduna

A wani labarin, 'yan bindigar da suka yi garkuwa da wasu mutane a Anguwan Bulus da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun kashe uku daga cikin su sannan sun yi barazanar kashe wasu har sai an biya kudin fansa.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kakakin yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da kisan yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Sabon hari: ‘Yan bindiga sun budewa jama'a wuta, sun hallaka wani adadi mai yawa

“Na amsa kiran waya daga wasu mutane uku a safiyar nan cewa an tsinci gawarwakin mutum uku a kauyen Dutse a wani waje a cikin jeji. An kwashe gawarwakin zuwa asibitin Saint Gerald Hospital. Muna kokarin tattaunawa da kwamandan yankin domin tabbatar da ganin wadanda ke tsare sun dawo lafiya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel