Bayan shafe kwanaki 18 a hannun yan bindiga, basaraken Abuja ya samu yanci

Bayan shafe kwanaki 18 a hannun yan bindiga, basaraken Abuja ya samu yanci

  • Sarkin Bukpe da ke yankin Kwali na birnin tarayya Abuja da aka sace, Mai Martaba Alhaji Hassan Shamidozhi, ya samu yanci
  • Kamar yadda basaraken ya bayyana, an sako shi tare da wasu talakawansa biyu a ranar Asabar, 16 ga watan Afrilu
  • Ya ce hakan ya yiwu ne bayan yan uwa da abokan sun hada naira miliyan hudu inda suka biya masa kudin fansa

Abuja - Basaraken garin Bukpe da ke yankin Kwali na birnin tarayya Abuja da aka sace, Mai Martaba Alhaji Hassan Shamidozhi, ya samu yancinsa bayan shafe kwanaki 18 a tsare, PM News ta rahoto.

Legit Hausa ta tattaro yadda masu garkuwa da mutane suka farmaki fadar sarkin Bukpe sannan suka sace shi tare da wasu mazauna garin biyu.

An saki sauran wadanda aka sace tare da shi bayan an biya kudin fansa naira miliyan 2.5.

Kara karanta wannan

Wa'adin awa 24 ga dangin basaraken Abuja: Ko ku biya N6m ko kuma kunsan sauran, inji 'yan bindiga

Bayan shafe kwanaki 18 a hannun yan bindiga, basaraken Abuja ya samu yanci
Bayan shafe kwanaki 18 a hannun yan bindiga, basaraken Abuja ya samu yanci Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Basaraken wanda ya zanta da jaridar Daily Trust a fadarsa a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu, ya ce wadanda suka sace shi sun sake shi tare da talakawansa biyu da misalin karfe 6:12 na ranar Asabar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa iyalansa, yan uwa da abokan arziki sun hada naira miliyan 4 bayan zazzafan tattaunawa da yan bindigar.

Ya ce jim kadan bayan biyan kudin fansar, masu garkuwa da mutanen suka jagorance shi da talakawan nasa biyu zuwa wani daji da ke kusa da kauyen Zokutu, inda suka yi tattaki na wasu awowi kafin suka billo hanyar Abaji-Toto, inda aka kwashe su a mota zuwa gida.

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan birnin tarayya, DSP Adeh Josephine, ba tukun kan sakin basaraken.

Wa'adin awa 24 ga dangin basaraken Abuja: Ko ku biya N6m ko kuma kunsan sauran, inji 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Dan majalisa a Filato: An kashe makusantana fiye da 50 a harin 'yan bindiga

A wani labarin, mun kawo a baya cewa wadanda suka yi garkuwa da Hassan Shamidozhi, basaraken garin Bukpe da ke yankin Kwali na birnin tarayya Abuja, sun ba iyalansa wa’adin awa 24 su kawo naira miliyan 6 ko kuma su rasa shi.

Yan bindigar sun yi garkuwa da basaraken ne makonni biyu da suka gabata sannan suka nemi a biya kudin fansarsa naira miliyan 20.

Sai dai kuma, a jiya Alhamis, masu garkuwa da mutanen sun yi barazanar kashe basaraken idan har iyalansa suka gaza hada masu naira miliyan 6 a yau, jaridar The Guardian ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng