Da wa Allah ya hada ni: Wanda aka sace ya biya kudin fansa ya hadu da wanda ya sacesa a cikin gari

Da wa Allah ya hada ni: Wanda aka sace ya biya kudin fansa ya hadu da wanda ya sacesa a cikin gari

  • Matashi ya yi arangama da wanda yayi garkuwa da shi kuma ya sako shi bayan ya biya kudin fansa a yankin Idi-Ori da ke Abeokuta
  • Tuni matashin ya yi kururuwa inda jama'a suka taru tare da kama mai garkuwa da mutanen, sun daure shi tare da farfasa masa jiki har da yunkurin halaka shi
  • Da kyar 'yan sanda suka kwaci mai garkuwa da mutanen daga hannun jama'ar da suka ce basu yarda da 'yan sanda ba don za su iya sakinsa

Ogun - An yi kwarya-kwaryar dirama a ranar Litinin a yankin Idi-Ori da ke Abeoukuta a karamar hukumar Abeokuta ta arewa a jihar Ogun yayin da wani mutum ya gane wanda ya yi garkuwa da shi har ya biya shi kudin fansa.

Sai dai mai garkuwa da mutanen ya ci sa'a ta yadda ya tsallake rijiya da baya ba a kashe shi ba bayan da fusatattun mutane suka ritsa shi.

Kara karanta wannan

Duk magidancin cocina da ke dukan matarsa, sai na lakada masa duka, Fasto Suleman

Da wa Allah ya hada ni: Wanda aka sace ya biya kudin fansa ya hadu da wanda ya sacesa a cikin gari
Da wa Allah ya hada ni: Wanda aka sace ya biya kudin fansa ya hadu da wanda ya sacesa a cikin gari. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

Vanguard ta tattaro cewa, wanda ake zargin yana tsaka da shawagi a yankin yayin da mutumin ya gane shi.

A take kuwa mutumin ya yi kururuwa inda ya jaddada cewa wanda ake zargin ya karba kudin fansa bayan ya sace shi da wasu a yankin ne.

Wata ganau wacce ta bayyana sunanta da Olubukola, ta ce fusatattun matasan a Idi-Ori, sun kama matashin inda suka masa mugun duka.

Ta ce, "Sun daure hannayensa da kafafunsa. Suka masa duka tare da farfasa masa jiki. Sun so kone shi, cetonsa daya da ya zo shi ne bayyanar 'yan sanda da wuri daga yankin Lafenwa a Abeokuta.
"Da farko, fusatattun matasan ba su so bai wa 'yan sanda matashin ba. Sun ce ba su yarda da su ba. Tsoronsu kada a bada belinsa sai suka jaddada cewa suna da tabbacin mai garkuwa da mutane ne."

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun sace amarya ana gobe daurin aurenta a Kaduna

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce har yanzu zargin matashin ake yi kuma ana bincike a kansa.

Ya kushe yunkurin halaka shi da aka yi inda yace doka bata yarda da daukar mataki a hannu ba.

Kamar yadda Oyeyemi yace, ko da matashin ya kasance mai garkuwa da mutane, dole za a bankado abokan harkarsa.

"Na san yadda lamarin ya faru. Har yanzu wanda ake zargi yana hannunmu har sai mun kammala bincike. Saboda haka ne bai dace ba jama'a su dinga daukar doka a hannunsu. Ba kawai za ka kama mutum bane ka fara yunkurin halaka shi. Su bar mu muyi binciken da ya dace.
"Ko da mai garkuwa da mutane ne, ai ba shi kadai bane. Bincikenmu zai sa mu kama wasu. Daga nan ne za mu magance matsalar a yankin gaba daga. Jama'a su daina daukar doka a hannunsu," Oyeyemi yace.

Kara karanta wannan

Yafewa Nyame da Dariye ta jawo Jami’an EFCC, ICPC su na jifan Shugaban kasa da zargi

'Yan bindiga sun halaka basarake da wasu mutum 24, sun sace babura a Benue

A wani labari na daban, a daren ranar Litinin ne aka kashe wani basarake, Zaki Unongo Shaayange da wasu mutane 24 a wasu hare-hare uku da 'yan bindiga suka kai yankunan kananan hukumomin Logo, Tarka da Guma, na jihar Benue.

Vanguard ta ruwaito cewa, harin ya bar mutane da dama kwance a asibitoci da raunuka masu tsanani wanda suka samu daga harbin bindiga.

An tattaro daga wani shugaban al’umma, Cif Joseph Anawa, cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai kimanin shida sun tare hanyar Anyiin-Tse Kile a Ukemberagya na karamar hukumar Gaambetiev Logo a daren ranar Litinin da misalin karfe 7:15.

Asali: Legit.ng

Online view pixel