Karin bayani: Jirgin saman sojoji ya hatsari a Kaduna, jami'ai 2 sun mutu

Karin bayani: Jirgin saman sojoji ya hatsari a Kaduna, jami'ai 2 sun mutu

Rahotanni sun yawata kafafen yada labarai a Najeriya kan faduwar wani jirgin saman horar da sojoji

  • Rahoton ya ce, akalla mutane biyu suka mutu a hatsarin, wanda aka ce ya afku a cibiyar sojin saman Najeriya
  • Ya zuwa yanzu dai ba a samu jin ta bakin hukumar ba, amma wasu dangi sun shaida wa wakilinmu faruwar lamarin

A yammacin ranar Talata ne wani jirgin horar da sojojin saman Najeriya ya yi hatsari a garin Kaduna, Arewa maso Yammacin Najeriya.

Majiyoyi sun ce ana fargabar mutuwar matukan jirgin biyu da ke cikinsa yayin hatsarin, inji rahoton Leadership.

Hatsarin jirgin saman sojoji ya kashe jami'ai biyu a Kaduna
Da dumi-dumi: Jirgin saman sojoji ya fadi a Kaduna, jami'ai 2 sun mutu | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta shaida cewa, jirgin na Super Mushak na horar da jami'ai ya yi hatsari ne a cibiyar NAF ta Kaduna a lokacin da ya ke aikin horor da jami'an tsaron.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Kwankwaso ya lale N30m, ya sayi fom din takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP

Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Cdre Edward Gabkwet, bai amsa neman karin bayani daga majiya ba kan faruwar lamarin.

Wani dangin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Legit.ng Hausa cewa, daya daga cikin jami'an da ya rasu sunansa Leutenant Abubakar Alkali.

Sai dai bai yi wani karin bayani game da lamarin ba.

Wani rahoton da BBC Hausa ta fitar ya ce, majiya ta shaida cewa, matukin jirgin ne ya rasu a hadarin da har yanzu ba a samu karin haske a kai ba.

Shugaban hafsun sojojin kasan Najeriya ya mutu bayan watanni 4 a ofis

Labarin da muka wallafa a baya ya bayyana, cewa shugaban hafsun sojojin kasa na Najeriya, Laftana Janar Ibrahim Attahiru ya rasu jim kadan bayan hawa mukaminsa.

Mabanbantan rahotanni sun tabbatar mana da mutuwar babban sojan kasar wanda ya shiga ofis a karshen Junairun 2021. J

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

aridar PM News ta bayyana cewa Laftana Janar Ibrahim Attahiru ya mutu a sanadiyyar hadarin jirgin sama a ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.