Masu garkuwa da mutane sun sace amarya ana gobe daurin aurenta a Kaduna

Masu garkuwa da mutane sun sace amarya ana gobe daurin aurenta a Kaduna

  • An yi garkuwa da wata mai shirin zama amarya ana gobe daurin aurenta a yankin Sanga da ke jihar Kaduna
  • Wadanda suka sace amaryar mai suna Tina sun yi ram da ita ne yayin da take hanyarta na zuwa wajen gyaran gashi
  • An tattaro cewa tuni maharan suka tuntubi yan uwanta amma dai basu bukaci a biya kudin fansarta ba tukuna

Kaduna - Masu garkuwa da mutane sun sace wata matashiyar budurwa mai suna, Tina Moses, a ranar jajiberin aurenta a jihar Kaduna.

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa kamar yadda aka tsara, ya kamata a daura auren Tina da angonta Elisha Koje a ranar Asabar, 16 ga watan Afrilu a karamar hukumar Sanga da ke jihar.

Kara karanta wannan

Sabon hari: ‘Yan bindiga sun budewa jama'a wuta, sun hallaka wani adadi mai yawa

Masu garkuwa da mutane sun sace amarya ana gobe daurin aurenta a Kaduna
Masu garkuwa da mutane sun sace amarya ana gobe daurin aurenta a Kaduna Hoto: Linda Ikeji
Asali: UGC

A cewar Esther Attah Asheri, an sace kanwar mijinta Tina a ranar Juma’a a hanyarta na zuwa wajen gyaran gashi a garin Kaduna.

Ta ce:

“An yi garkuwa da kanwar mijina a garin Kaduna yau ne ya kamata ace ya zama ranar farin cikinmu domin a yau ne za a daura mata aure amma sai wasu mutane suka zabi mayar mana da shi ranar bakin ciki. Dan Allah ku tayamu da addu’a don dawowarta lafiya.”

Esther ta ci gaba da bayyana cewa wadanda suka yi garkuwa da ita sun tuntubi iyalan amma basu riga sun bukaci kudin fansa ba tukuna.

Yan bindiga sun yi garkuwa da Amarya ana gab da aurenta da wasu mutum 5 a Kaduna

A wani labari makamancin wannan, mun ji a baya cewa yan bindiga sun farmaki Anguwar Rigachikun, dake karamar hukumar Igabi, cikin garin Kaduna, sun sace wata budurwa dake shirin zama amarya da wasu mutum 5.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun tsare mai tsohon ciki, ta na kokarin nakuda, su na neman kudin fansa

Daily Trust ta tattaro cewa yan ta'addan sun kai hari yankin wanda ke kusa da Kasan Dam da misalin karfe 1:00 na daren ranar Laraba.

Maharan sun kutsa gida bayan gida suka zabi wasu mutane dake zaune a yankin, cikinsu harda Amarya mai shirin fara Amarci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel