Labaran garkuwa da mutane
An ruwaito yadda 'yan ta'adda suka kai sabon hari a Kaduna bayan da aka kashe shugabansu a wani yankin jihar. An jima ana samun hare-hare a jihar Kaduna.
‘Yan bindiga sun kashe daya daga cikin mutane bakwai da aka sace daga yankin Kuduru a Abuja bayan karbar naira miliyan 20, sun kuma yi barazanar kashe wasu.
Sojojin rundunar Operation Whirl Stroke sun yi nasarar kubutar da mutum 13 da aka yi garkuwa da su yayin da muyagun ke kan hanyar kai su jihar Adamawa daga Imo.
‘Yan sanda sun gurfanar da wasu mutum biyu a gaban Babbar Kotu kan zargin hadin baki don sace kanin gwamnan Bayelsa, Douye Diri tun a watan Nuwambar 2023.
Rundunar 'yan sandan jihar Neja ta tabbatar da cewa jami'anta sun samu nasarar halaka wani mai garkuwa da mutane, biyo bayan artabun da suka yi a jihar.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun toshe babban titin Gusau zuwa Sakkwato, su. yi awon gaba da matafiya daga motoci biyu da yammacin ranar Talata a yankin Maru.
Dakarun sojojin saman Najeriya da aka girke a Durbunde da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano sun kama wani babban mai garkuwa da mutane mai suna Isah Abdul.
Miyagun ƴan bindiga sun kuma yin garkuwa da mutane masu yawa a hanyardu ta zuwa Lokoja, babban birnin jihar Kogi, sun kira wsya sun nemi kuɗin fansa.
Sai an ba Gwamnoni ‘Yan sanda a jihohi idan ana son saukin rashin tsaro. A wuraren da gwamnonin nan suka tashi tsaye, Uba Sani ya ce an fara samun saukin tsaro.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari