Mutane Sun Fusata, Sun Bazama Kan Babban Titi Suna Ƙone-Ƙone Kan Hare-haren Ƴan Bindiga

Mutane Sun Fusata, Sun Bazama Kan Babban Titi Suna Ƙone-Ƙone Kan Hare-haren Ƴan Bindiga

  • Fusatattun mazauna kauyen Wurma a karamar hukumar Kurfi sun tsohe babban titin Katsina-Dutsinma kan hare-haren ƴan bindiga
  • Masu zanga-zangar sun hana matafiya wucewa, lamarin da ya tilasta wa ababen hawa canza hanya domin tafiya garuruwan da suka nufa a sassan jihar
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, ASP Aliyu, ya ce zai tuntuɓi DPO na Kurfi gabanin ya yi magana a hukumance

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Mutanen kauyen Wurma a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina sun fara ƙone-ƙone tare da toshe babban titin Katsina-Dutsinma ranar Jumu'a, 1 ga watan Maris.

Mazauna kauyen sun toshe titin ne domin nuna fushinsu kan yadda ƴan bindiga suka matsa musu da kai hare-haren ta'addanci da kashe-kashen rayuka.

Kara karanta wannan

Rigima ta ƙara zafi a APC yayin da dakarun ƴan sanda suka ƙwace iko da sakateriya a jihar Arewa

Gwamna Umaru Radda.
Mazauna Kauye Sun Toshe Babban Titin Katsina Zuwa Dutsinma Kan Hare-Haren Yan Bindiga Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda Ph.D
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa zanga-zangar da tilastawa motoci da sauran matafiya canza hanya, sun koma bin hanyoyin jeji da suka haɗa Dutsinma da sassan Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mai suna, Abdulkarim, ɗaya daga cikin ƴan kauyen da suka fito zanga-zanga ya ce a kwanaki hudu da suka shiga, ƴan bindiga suna shiga garinsu babu ɗaga ƙafa.

A cewarsa, hare-haren ta'addanci da ƴan bindiga ke yawan kai musu ga jefa su cikin rayuwar tsoro da fargabar abin ka iya faruwa a ko wane lokaci.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Yayin da muka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Aliyu, ya ce zai nemi ƙarin bayani daga DPO na Kurfi kafin ya yi magana.

Sai dai har zuwa lokacin da muka haɗa muku wannan rahoton, ba a samu wani karin bayani kan lamarin ba daga rundunar ƴan sanda.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: Asirin wasu ƴan bindiga 15 ya tonu, sun fara sakin bayanai a jihar Arewa

Haka nan kuma har zuwa misalin karfe 2:00 na rana, jami'an tsaron da suka je wurin ba su taka kara sun karya ba, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Fusatattun mazauna kauyen sun yi amfani da wannan dama wajen hana ababen hawa wucewa da tilastawa matafiya canza hanya.

Sojoju sun samu galaba kan ƴan ta'adda

A wani rahoton na daban Jami'an rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar halaka mayakan Boko Haram/ISWAP uku a yankin tafkin Chadi.

Sojojin sun kuma kwato muggan makamai da kayan aikin ƴan ta'addan a samamen da ya ƙara nakasa su ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel