Yan Sanda Sun Cafke Wasu Dattawa 2 da Kokarin Sace Kanin Gwamnan PDP, Sun Shiga Ha’ula’i Tun Yanzu

Yan Sanda Sun Cafke Wasu Dattawa 2 da Kokarin Sace Kanin Gwamnan PDP, Sun Shiga Ha’ula’i Tun Yanzu

  • ‘Yan sanda sun gurfanar da wasu kan zargin hadin baki don sace kanin gwamnan Bayelsa, Douye Diri tun a watan Nuwamba
  • Yayin gurfanar da wadanda ake zargin a yau Juma’a 23 ga watan Faburairu sun musanta aikata laifin da ake tuhumarsu
  • An gurfanar da mutanen ne biyu a Babbar Kotun Kaima da ke birnin Yenagoa kan zargin kokarin sace Mista Ebi Ayama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bayelsa – Rundunar ‘yan sanda ta kama wasu mutane biyu da hadin baki don yin garkuwa da kanin gwamnan jihar Bayelsa.

Ayama wanda aka fi sani da Americana dan uwa ne ga Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Wasu ba su tsallake ba da aka tantance mutum 17 da Tinubu ya ba mukami a majalisa

An cafke mutum biyu da kokarin sace kanin gwamnan PDP
An gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu don girbar abin da suka shuka. Hoto: Douye Diri.
Asali: Facebook

Menene ake zargin mutane da aikatawa?

Wadanda ake zargin da hada makarkashiya don sace Americana sun hada da Lucky Oghenebrume mai shekaru 53 da Omobowho Okpowodo mai shekaru 52.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar ta ce an kama mutanen ne guda biyu a watan Nuwambar 2023 a yankin Mbiama da ke jihar Rivers.

Ta ce nasarar kama wadanda ake zargin ya na da nasaba da bayanan sirri da suka samu daga mutane da kuma binkicen tsaro.

Sai dai wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin da ake tuhumarsu a kai na kisa yunkurin sace Americana, The Guardian.

Wane mataki kotun ta dauka?

Mai gabatar da kara ya ce Ogbenebrume shi ne ya kitsa sace wani mutum mai suna Fyneman a Sagbama da ke jihar inda ya biya shi kudin fansa miliyan 50.

Dan sandan da ke gabatar da karar ya ce mutum na biyu, Omobowho makanike ne da Americana ya kai gyara garejinsa.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ‘sojojin bogi’ a Legas, an gano abin da zai faru da su

Omobowho ya tabbatar da cewa ya ji lokacin da suke kulla yadda za su sace Ayama a kan hanyarsa daga karamar hukumar Ekeremor.

Alkalin kotun, Timipre Songi daga bisani ya dage sauraran karar har zuwa ranar 27 ga watan Faburairun da muke ciki.

An kaure tsakanin Hausawa da Yarbawa a Legas

Kun ji cewa an samu rasa rai bayan rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Oluwole da ke jihar Legas.

Rikicin ya faru ne a daren jiyar Alhamis 22 ga watan Faburairu yayin da wani Abbey ke kokarin raba Hausawa fada a kasuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel