Innalillahi: Ƴan bindiga Sun Kai Ƙazamin Hari Kan Matafiya, Sun Tafka Mummunar Ɓarna a Jihar Arewa

Innalillahi: Ƴan bindiga Sun Kai Ƙazamin Hari Kan Matafiya, Sun Tafka Mummunar Ɓarna a Jihar Arewa

  • Kimanin mako biyu bayan abinda ya faru, ƴan bindiga sun ƙara sace matafiya da dama a kan babban titin zuwa Lokoja a jihar Kogi
  • Wani mai buƙata ta musamman da matarsa ke cikin waɗanda aka sace, ya ce masu garkuwan sun kira sun nemi makudan kuɗin fansa
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda, SP William Aya, ya ce bai da masaniya kan harin amma zai bincika kafin ya yi magana a hukumance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da matafiya da dama a jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya.

Maharan sun yi awon gaba da matafiya mutum 9 a ƙauyen Oshokoshoko da ke kan titin Kabba/Obajana/Lokoja a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Wasan karshe na AFCON: Gaskiyar batu kan bidiyon da ke zargin golan Ivory Coast da sanya guraye

Yan bindiga sun ƙara sace matafiya a Kogi.
An kuma, yan bindiga sun sake yin garkuwa da matafiya masu yawa a jihar Kogi Hoto: Nigerian Folice Force
Asali: Twitter

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar din da ta gabata kuma an gano cwwa wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da direban motar, dalibai biyu, da wasu shida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin ya zo ne bayan kimanin makonni biyu da aka yi garkuwa da wasu matafiya da ke kan hanyarsu ta zuwa Abuja bayan sun fito daga Gabashin kasar nan.

Yadda ƴan bindiga suka kai sabon hari

Leadership ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar da ta wuce da misalin karfe 5 na yamma a lokacin da fasinjojin suka taso daga Kabba zuwa Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Wani mai naƙasa, Elupo Eliazer, wanda matarsa ke cikin waɗanda aka yi garkuw ada su, ya ce maharan sun kira waya a karon farko suka nemi Naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Abuja: Mota ta murkushe barawo bayan fauce kayan abincin wata mata, ya shiga kakani-kayi

Amma mutumin ya ƙara da cewa daga bisani masu garkuwan sun yi rangwame, suka dawo N2.6m bayan doguwar tattaunawa.

A kalamansa, Eliazer ya ce:

"Da ni da matata mun shirya tafiya domin halartar taron cocin mu a Lokoja amma sai na yanke shiga wata motar daban saboda ta farko ta cika, ba zata ɗauke mu ba, ba don haka ba da nuna tare da ita.

Ya ce motar da matarsa ke ciki tana gaban tasu kuma maharan sun yi awon gaba da su zuwa cikin daji kafin su ƙarisa wurin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), SP William Aya, ya ce bai da masaniya kan faruwar lamarin amma zai bincika sannan ya yi magana.

Ƴan bindiga sun tafka ɓarna a Neja

A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja, sun tafka mummunar ɓarna ranar Lahadi.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun ƙona gidaje akalla 30 da kayan binci, kana suka yi awon gaba da mutane masu yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel