Yan Bindiga Sun Toshe Fitaccen Titi a Arewacin Najeriya, Sun Sace Matafiya Masu Ɗumbin Yawa

Yan Bindiga Sun Toshe Fitaccen Titi a Arewacin Najeriya, Sun Sace Matafiya Masu Ɗumbin Yawa

  • Yan bindiga sun tare motoci a kan babban titin Gusau zuwa Sokoto, sun sace matafiya sama da 20 da yammacin ranar Talata
  • Wani mazaunin yankin ya ce hare-haren ƴan bindiga na ƙara kamari saboda a yanzu tsohe hanyar da suke yi ya zama na kullum-kullum
  • Ya roki gwamnati ta taimaka ta girke dakarun sojoji a kewayen yankin, inda ya yi ikirarin akwai wani kauyen a titin da ke ɓoye ƴan ta'adda

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya 26 a kan fitaccen titin nan da ya tashi daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara zuwa Sakkwato.

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigan sun sa get suka tsohe hanya a kusa da ƙauyen Kwaren Kirya da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki kan bayin Allah, sun kashe mutane tare da tafka ta'asa mai ban tausayi

Sufetan ƴan sanda na ƙasa, IGP Kayode.
Yan bindiga sun toshe babban titin Gusau Zuwa Sokoto, Sun Sace matafiya masu yawa Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Maharan sun tattara dukkan fasinjojin cikin motar bas mai cin mutum 18 da kuma motar Volkswagen golf, suka yi awon gaba da su zuwa cikin jeji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hare-haren ƴan bindiga ya zama ruwan dare a titin

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro ya shaidawa Channels Tv cewa lamarin na kara ta'azzara saboda a kullum 'yan bindiga suna tare hanya.

Mutumin ya ce:

"Yanzu da nake magana da ku ƴan bindiga sun ƙara tare hanya a kan babban titin mintuna 30 da suka wuce. Sun kwashe fasinjojin bas 18 da motar Golf.
"Lamarin ƙara ta'azzara yake yi kullum saboda yanzun kusan kowace rana sai mutanen nan sun tare hanya."

Ana zargin mutanen wani kauye na ɓoye ƴan bindiga

Ya kuma nuna damuwarsa kan wani kauye mai suna Balge da ke kan titin Gusau-Sokoto, wanda ya yi ikirarin suna bai wa ƴan bindiga mafaka.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka halaka bayin Allah da yawa a garuruwa 5 a jihar Arewa

Haka nan kuma ya yi kira ga gwamnati ta tura jami'an tsaro zuwa kewayen yankin domin su taka wa ƴan bindigan birki.

Ya ƙara da cewa:

"Akwai wani ƙauye idan ka wuce Kwaren Kirya wanda ake kira Balge, kashi 80 na mutanen da ke zaune a garin ƴan bindiga ne.
"An taɓa fatattakar su daga wurin amma mafi akasarin mutanen kauyen duk ƴan bindiga ne, muna rokon gwamnati ta taimake mu, ta girke dakarun sojoji a kewayen yankin."

Har kawo yanzu da muke haɗa muku wannan rahoton, rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ba ta ce komai ba kan sabon harin.

Ƴan bindiga sun kai hari a Katsina

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun kashe bayin Allah har mutum shida yayin da suka kai farmaki kauyuka 3 a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Mazauna yankin sun tabbatar da cewa maharan sun aikata wannan ta'asa jiya Litinin kuma sun yi awon gaba da mutane masu yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel