Labaran garkuwa da mutane
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari a dakin kwanan dalibai na jami'ar tarayya da ke Wukari a jihar Taraba. Rahotanni sun tabbatar da aukuwar lamarin.
Rahotanni sun nuna cewa wasu tsagerun ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai masu yawa yayin da suka hanyar komawa gida jihar Delta daga Kuros Riba.
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai sama da 100 na makarantar kauyen Kuriga da aka ceto daga hannun ƴan bindiga kwanan nan.
Bishof Mathew Kukah, babban malamin cocin katolika a jihar Sakkwato ya dira kan wasu manyan ƴan Najeriya da ke haɗa kai da ƴan bindiga masu satar dalibai.
Wani shafin yanazar gizo mai tsage gaskiya ya tabbatar da cewa ikirarin cewa an yi awon gaba da mai ɗakin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ba gaskiya bane.
Farfesa Babagana Umaru Zulum ya ce shirin aminci a makarantu da suka kaddamar a Borno tun shekaru bakwai zuwa takwas da suka wuce yana aiki yadda ya kamata.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya koka kan yawaitar ayyukan masu garkuwa da mutane. Ya bayyana su a matsayin 'yan ta'adda wadanda za a kawo karshensu.
Wasu maharan sun yi garkuwa da matan aure 12 da namiji ɗaya, sun kwashi dukiyar bayin Allah mai ɗumbin yawa a karamar hukumar Dutsinma a jihar Katsina.
Wani ɗan bindiga ya bude shafi a dandalin TikTok, inda ya ke baje kolin irin maƙudan kuɗaɗe da makaman da tawagarsa ta tara. Lamarin da ya jawo cece-kuce.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari