Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Makaranta, Sun Dauke Yaran Firamare

Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Makaranta, Sun Dauke Yaran Firamare

  • Tsagerun 'yan bindiga sun kai hari makarantar firmare ta LEA, a garin Kuriga, karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna
  • An rahoto cewa maharan sun yi harbe-harbe tare da sace dalibai da ake tunanin yawansu ya kai 100 a harin
  • Haka kuma, shugabar makarantar da wasu ma'aikata suna cikin wadanda 'yan bindigar suka tasa keyarsu zuwa cikin jeji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

An samu tashin hankali a garin Kuriga da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, lokacin da wasu 'yan bindiga suka farmaki makarantar firmare ta LEA, Kuriga (1) tare da sace dalibai da dama.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, ba a san adadin daliban da aka sace ba zuwa yanzu, amma mazauna yankin sun ce sun kai kimanin su 100.

Kara karanta wannan

Bashin dalibai: Tinubu ya bayyana ranar da zai kaddamar da shirin ba dalibai rancen kudi

'Yan bindiga sun farmaki makarantar firamare a Kaduna
Kaduna: 'Yan bindiga sun kai hari makarantar firamare a Kaduna Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa shugaban malamai na makarantar da wasu ma'aikata suna daga cikin wadanda aka sace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta'adin 'Yan bindiga a Kaduna

An kuma tattaro cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 8:20 na safiya, jim kadan bayan bude makarantar a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris.

Makarantar sakandaren ta koma cikin garin Kuriga 'yan shekaru da suka gabata saboda rashin tsaro, inda suka bar tsohon gininsu da ke wajen garin.

Mazauna Kaduna sun yi tsokaci

Wani mazaunin yankin, Shittu ya tabbatar da faruwar lamarin, cewa yawancin daliban sun tsere daga ajujuwansu yayin da suka hango 'yan bindigar a harabar makarantar.

Wani Lawal Kuriga ma ya tabbatar da cewa an tasa keyar mutanen da aka sace zuwa cikin jeji.

Babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar kasancewar kwamishinan ma'aikatar tsaron jihar, Samuel Aruwan, bai amsa sakon da aka tura masa ba zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Halin kunci: 'Yan sanda da hukumar NEMA sun dauki mataki yayin da ake kai farmaki rumbunan abinci

Haka kuma, ba a samu jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ba, bai amsa sakon da aka tura masa ba.

An sace mutum 60 a Zamfara

A wani labarin kuma, mun ji cewa an yi awon gaba da dimbin mutane sakamakon mummunan harin da tsagerun yan bindiga suka kai a garin Rimi, a karamar hukumar Bakura jihar Zamfara, ranar Juma'a.

Kwamishanan labaran jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, ya tabbatar da hakan ranar Juma'a. A cewarsa, an yi garkuwa da kimanin mutum 60 amma jami'an tsaro basu tabbatar da adadin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel