Yan Sanda da Dakarun Sojoji Sun Yi Wa Ƴan Bindiga Rubdugu, Sun Samu Gagarumar Nasara a Arewa

Yan Sanda da Dakarun Sojoji Sun Yi Wa Ƴan Bindiga Rubdugu, Sun Samu Gagarumar Nasara a Arewa

  • Ƴan sanda da sojoji sun ceto matafiya 11 da ƴan bindiga suka sace daga motoci biyu a jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, SP William Aya, ya ce jami'an tsaron sun kai ɗauki bayan samun rahoton sace fasinjojin jiya Lahadi
  • Kwamishinan ƴan sanda, CP Bethrand Onuoha, ya yabawa jami'an tsaron bisa wannan nasara da suka samu kan miyagu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Rundunar ƴan sanda ta jihar Kogi da haɗin guiwar dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su a jihar Kogi.

Wannan nasara na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, SP William Aya, ya fitar ranar Litinin, Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama ɗaliban fitacciyar jami'ar Arewa bisa zargin kashe rayukan bayin Allah

Yan sanda da sojoji sun ceto mutim 16 a Kogi.
Yan sanda sun ceto matafiya 16 da ƴan bindiga suka sace a jihar Kogi Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Aya ya ce dakarun jami'an tsaron sun fita Operation ceto ne bayan samun rahoton sace matafiya 11 daga motar Bas da fasinjoji 5 daga motar Sienna a titin Ette-Enugu-Ezike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Leadership ta tattaro cewa ƴan bindiga sun tattara fasinjojin sun yi awon gaba da su a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2025.

SP Aya ya ce:

"Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Kogi da haɗin guiwar sojoji daga jihar Enugu suka kai ɗauki cikkn gaggawa kuma suka kubutar da baki ɗaya waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya."

Mai magana da yawun yan sanda ya kara da cewa "jami'ai na ci gaba da kokarin cafke wadanda ake zargin da aikata wannan ta'asa domin su fuskanci hukunci daidai da abinda suka aikata."

CP ya yaba da wannan nasara

Kwamaishinam ƴan sandan jihar Kogi, Bethrand Onuoha, ya yabawa dakarun tsaron bisa wannan gagarumar nasarar da suka samu kan ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

Jama'a sun daka wa tirelar kayan abinci wawa a jihar Katsina? An gano gaskiyar abinda ya faru

Ya nanata kudirin rundunar ƴan sanda na ci gaba da kai hare-hare kan masu aikata muggan laifuka a jihar.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro haɗin kai wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin su.

An kama ɗaliban ATBU

A wani rahoton kuma Yan sanda sun kama ɗalibai 2 na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi bisa zargin suna da hannun a kisan mutum biyu.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Ahmad Wakil, ya ce sun kuma kama ƙarin wani mutum ɗaya mai alaka da kisan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel