Yan Bindiga Sun Kashe Mazaunin Abuja Bayan Karbar Naira Miliyan 20, Sun Kuma Yi Barazanar Kashe Wasu

Yan Bindiga Sun Kashe Mazaunin Abuja Bayan Karbar Naira Miliyan 20, Sun Kuma Yi Barazanar Kashe Wasu

  • Yan bindiga sun kashe wani mazaunin Abuja wanda aka yi garkuwa da shi tare da wasu mutane a karshen watan Disambar 2023
  • Wata majiya daga iyalan mamacin ta shaida cewa sun kai wa 'yan bindigar naira miliyan 20, kayan abinci da sauran su amma suka kashe shi
  • Majiyar ta kuma ce 'yan bindigar sun yi barazanar kashe sauran mutane shida da ke hannun su idan ba a biya naira miliyan 230 ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - ‘Yan bindiga sun kashe daya daga cikin mutane bakwai da aka sace daga yankin Kuduru a babban birnin tarayya (FCT).

‘Yan bindigar sun kai farmaki yankin inda suka yi awon gaba da mutanen a ranar 28 ga watan Disamba, 2023.

Kara karanta wannan

Yan daba sun yi yunƙurin kutsawa kasuwar Jos don satar kayan abinci, jami'an tsaro sun dauki mataki

Rundunar 'yan sanda ta magantu kan rahoton kashe mutumin
Rundunar 'yan sanda ta magantu kan rahoton kashe mutumin. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Daily Trust cewa wanda aka kashen, Olayinka Ogunyemi, an kashe shi ne bayan da iyalansa suka gaza biyan naira miliyan 290.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun kira waya a ranar Juma’a inda suka sanar da kisan da suka yi wa Ogunyemi, wanda injiniyan gine-gine ne.

Yan bindigar sun yi barazanar kashe mutum shida

“Yan bindigar sun yi barazanar kashe yaro mai shekara daya da rabi, ‘yan uwa biyu, mace mai juna biyu da maza biyu da suka rage a hannunsu idan har ba a bayar da naira miliyan 230 kudin fansa ba.
“An biya naira miliyan 23, an aika da abinci da sauran kayayyakin da suka nema amma babu wani daga cikin mutanenmu da aka sako."

Majiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ‘yan sanda da sojoji da su kara kaimi wajen ganin sun ceto mutanen domin 'yan bindigar sun ce suna cike da fushin Najeriya.

Kara karanta wannan

Sanata Sani ya fadi mafita 1 da Musulmi da Kiristoci zasu runguma domin farfado da naira

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan FCT, Adeh Josephine, ya ce: “Ba ni da masaniyar faruwar lamarin.”

Jami'an EFCC sun cafke 'yan canjin kudi a Abuja, Kano da Oyo

A wani labarin, jami'an hukumar EFCC sun kai sumame kasuwar 'yan canji ta jihohin Kano da Oyo da kuma babban birnin tarayya Abuja.

A yayin sumamen, jami'an sun cafke 'yan canji da dama wadanda ake zargin su ne ke haddasa faduwar darajar Naira da tsadar dala a kasuwar canji ta kasar.

Wannan ya biyo bayan da gwamnatin tarayya ta bayar na kama masu hannu a faduwar darajar Naira da boye kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel