Sojojin Najeriya Sun Kai Samame Kan Ƴan Bindiga, Sun Samu Gagarumar Galaba a Jihar Arewa

Sojojin Najeriya Sun Kai Samame Kan Ƴan Bindiga, Sun Samu Gagarumar Galaba a Jihar Arewa

  • Sojojin rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS) sun samu babbar nasara a wani samame da suka kai kan ƴan bindiga a jihar Benuwai
  • Kwamandan rundunar, Manjo Janar Sunday Igbinomwanhia, ya ce dakarun sun yi nasarar ceto mutane 12 da aka yi garkuwa da su a hanyar kai su Adamawa
  • Ya ce sojojin da ke karƙashinsa na ci gama matsin lamba ga yan bindiga, ƴan ta'adda da sauran masu aikata muyagun laifuka a Benue, Taraba da Nasarawa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Dakarun sojojin rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS) sun kuɓutar da matafiya 12 da aka yi garkuwa da su a jihar Benuwai.

Sojojin sun ceto mutanen ne yayin da ake kan hanyar kai su jihar Adamawa daga jihar Imo dake Kudu maso Gabashin Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Sabuwar annoba ta kashe ma’aikatan lafiya uku da marar lafiya a asibitin sojin Najeriya

Dakarun sojin Najeriya.
Sojojin Najeriya Sun Ceto Mutum 12 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Benue Hoto: HQ Nigeria Army
Asali: Getty Images

Kwamandan rundunar OPWS, Manjo Janar Sunday Igbinomwanhia, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Makurdi ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce dakarun sojin da ke karkashinsa sun ci gaba da zafafa kai hare-hare kan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da sauran miyagun mutane a jihohin Binuwai, Nasarawa da Taraba.

Yadda sojoji suka gano masu garkuwa a motar bas

Ya ce a wani samame da sojojin sashi na 1 suka kai ranar 21 ga Fabrairu, 2024, a kauyen Jootar, karamar hukumar Ukum, sun ceto mutane 12 da aka yi garkuwa da su, wadanda ke hanyar Adamawa daga jihar Imo.

Igbinomwanhia ya yi bayanin cewa masu garkuwan sun yi amfani da shingen binciken ƴan sandan da aka daina amfani da shi wajen aikata wannan ɗanyen aiki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu yayin da sojoji suka kai samame cikin daji a jihar Arewa

A cewarsa, ƴan bindiga na ganin dakarun sojojin OPWS da ƙarfin luguden wuta, nan take suka arce suka bar mutanen da suka sato da nufin kai su Adamawa daga Imo.

"Sojoji sun kwato motar bas mai ɗaukar fasinja 18 mallakin kamfanin sufurin Taraba Express International mai lambar rijista GKA-371XA daga hannun masu garkuwa."

Su wa aka ceto daga hannun ƴan bindiga?

Mutanen da sojin suka ceto sun haɗa da Sule Abu, Misis Ashie Shuaibu, Suleiman Abdullahi, Zainab Salau, Muritala Yussuf, da Zainab Saidu.

Sauran kuma sune, Hammed Mamud, Usman Ali, Nura Abubakar, Mohammed Aliyu, Felicia Asusis, da kuma Jacob Nathaniel, rahoton Daily Post.

Insufekta ya rasa ransa a bakin aiki

A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun yi kwantan ɓauna, sun bude wa tawagar jami'an ƴan sanda wuta yayin da suke bakin aiki a shingen bincike a jihar Ribas

Yayin wannan farmaki, babban jami'an ɗan sanda da ya kai matakin insufekta ya rasa rayuwarsa, sannan jami'an sun sheƙe ɗaya daga cikin ƴan bindigar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel