Labaran garkuwa da mutane
Kasa da mako daya da 'yan bindiga suka kai hari yankin Dutse da ke Bwari, babban birnin tarayya Abuja, 'yan bindigar sun sake kai wani sabon harin a daren Talata.
Tsagerun ƴan bindiga sun kai farmaki kan matafiya a babban titin Abuja zuwa Kaduna, sun kashe wani direba sannan sun tafi da mutim biyu zuwa cikin daji.
Wata matar aure mai dauke da juna biyu ta haihu a cikin daji a hannun masu garkuwa da mutane bayan sun sace ta a jihar Enugu. Ta haifi jariri namiji.
Rahotanni daga jihar Zamfara sun nuna cewa wasu ƴan uwan amarya sun taru sun kashe ɗan bindiga ɗaya kuma sun kwato bindigu a titin Talatan Mafara zuwa Gusau.
Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta kama wasu mutum uku da suka yi wa kawun ɗaya daga cikinsu barazanar garkuwa, suka karɓi fansar Naira miliyan biyu.
Rahotanni sun nuna cewa wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kai farmaki garin Dutse da ke babban birnin tarayya Abuja inda suka yi garkuwa da mutane 5.
An kama wata mata mai shekara 40 da take ‘satar’ kanana yara. NAPTIP ta sashen Benin, ta ce sunan matar da aka kama Ikejimba Maryvianney kuma tana karyar Fasto ce.
Wani luguden wuta da aka yi ya hallaka mutane da-dama a wani kauye da ke jihar Zamfara. Hakimin Dogan Daji a Muradun ya ce mutanensu aka kashe ba 'yan bindiga ba.
Miyagun ƴan bindiga sun kai sababbin hare-hare a kauyukan Batsari da Malumfashi a ranaku daban-daban a makon nan, sun sace mutane da dama a jihar Katsina.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari