Tinubu Ya Fadi Kudin Fansan da Gwamnatinsa Za Ta Biya a Ceto Daliban da Aka Sace a Kaduna

Tinubu Ya Fadi Kudin Fansan da Gwamnatinsa Za Ta Biya a Ceto Daliban da Aka Sace a Kaduna

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan ɗaliban da ƴan bindiga suka je har cikin makaranta suka sace a jihar Kaduna
  • Tinubu ya bayyana cewa ko sisin kwabo ba za a biya miyagun ƴan bindigan ba domin a kuɓutar da yaran daga hannunsu
  • Ya jaddada umarninsa ga jami'an tsaron ƙasar nan da su tabbatar cewa sun ceto yaran daga hannun tsagerun cikin ƙoshin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce ba za a biya kuɗin fansa ba domin ceto ɗaliban da aka sace a ƙauyen Kuriga da ke jihar Kaduna.

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 12 ga watan Maris a wurin taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa, a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton gidan talabijin na Channels tv.

Kara karanta wannan

Batun ba dalibai rance ya bi ruwa: Gwamnatin Tinubu ta dakatar da shirin aron kudin karatu

Shugaba Tinubu ya magantu kan daliban da aka sace a Kaduna
Shugaba Tinubu ya ce ko sisi ba za a biya ba wajen ceto daliban Kaduna Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Muhammad Idris, shi ne ya bayyana matsayar shugaban ƙasan yayin da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan bayan kammala taron na FEC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naira nawa Tinubu zai biya a ceto ɗaliban?

Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya kuma sake jaddada umarninsa ga jami’an tsaro da su tabbatar sun ceto yaran tare da dawo da su gidajensu cikin ƙoshin lafiya, rahoton da jaridar The Nation ta tabbatar.

Idris ya kuma ce shugaban ƙasar na nan kan bakansa na adawa da biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane.

Ministan ya kuma yi nuni da cewa wannan gwamnatin mai ci ta ƙuduri aniyar magance matsalar garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka a ƙasar nan.

A cewarsa, a ƙarƙashin wannan gwamnati mai ci ba za a amince da yin garkuwa da mutane ba musamman yin awon gaba da gomman mutane.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fayyace gaskiya kan masu zargin Buhari ne ya lalata Najeriya

Satar mutane: Atiku ya caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi martani kan sace-sacen da ƴan bindiga ke yi a ƙasar nan.

Ɗan takarar shugaban ƙasan a ƙarƙashin inuwar jam'iyysr PDP a zaɓen 2023, ya zargi Shugaba Tinubu da gazawa wajen kare rayuka da dukiyar al'ummar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel