Kano: Hukumar NSCDC Ta Kama Dattijo Mai Shekaru 85 da Laifin Garkuwa da Karamin Yaro

Kano: Hukumar NSCDC Ta Kama Dattijo Mai Shekaru 85 da Laifin Garkuwa da Karamin Yaro

  • Hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta kama wani dattijo mai shekaru 85 ya sace yaron makwafta a Rimin Kebe da ke Kano
  • An yi zargin dattijon ya sace yaron tare da kai shi ajiya wajen abokinsa da ke Hotoro, inda shi kuma abokin ya tona asirin dattijon
  • Kakakin NSCDC, Abdullahi, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yi yunkurin guduwa amma jami’an hukumar suka damke shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta kama wani dattijo mai shekaru 85 mai suna Ibrahim Usman da ake zargi da yin garkuwa da mutane a Kano.

An kama Usman ne a unguwar ‘Yar’adua da ke Rimin Kebe a karamar hukumar Ungoggo bisa zargin satar wani yaro dan shekara 3 a unguwarsu.

Kara karanta wannan

Tsohon sarkin Kano, Sanusi ya fashe da kuka a wajen makokin Herbert Wigwe, bidiyo

Hukumar tsaron farar hula (NSCDC)
Dattijo da ya yi garkuwa da karamin yaro a Kano ya shiga hannu. Hoto: @NSCDCrops
Asali: Twitter

Abokin dattijon ne ya fallasa shirinsa - Abdullahi

The Punch ta ruwaito cewa kakakin hukumar NSCDC a jihar, Ibrahim Idris Abdullahi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi ya ce:

"“Wanda ake zargin (Ibrahim Usman), ya sace yaron dan shekara 3 kuma ya yi yunkurin boye shi a gidan abokinsa da ke sha tale-talen Hotoro a jihar Kano.
“Abokin nasa ya ki ya karbi ajiyar yaron, kuma ya yanke shawarar sanar da mazauna unguwar Rimin Kebe in da dattijon ya sato yaron."

NSCDC za ta gurfanar da dattijon gaban kotu

Kakakin NSCDC ya yi nuni da cewa wanda ake zargin ya yi yunkurin guduwa amma jami’an hukumar reshen Ungoggo suka damke shi.

A rahoton Leadership, Abdullahi ya jaddada cewa dattijon ya karbi lambar wayar mahaifin wanda ya yi garkuwa da shi watanni biyu da suka wuce amma bai kira shi sau daya ba.

Kara karanta wannan

Bayan Dangote, jama'a sun tare motar BUA, an wawushe kayan abinci ana tsakiyar yunwa

Ya kuma bayyana cewa hukumar NSCDC ta fara gudanar da bincike kan lamarin kuma za ta gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu da zaran ta kammala.

NSCDC ta kama matashin da ya kashe mahaifinsa

A wani labarin har ila yau daga jihar Kano, jami'an hukumar NSCDC sun kama wani matashi da ake zargin shi ne ya kashe mahaifinsa a karamar hukumar Gwale da ke jihar Kano.

Legit Hausa ta ruwaito cewa matashin mai suna Alkasim na fama da lalurar tabin kwakwalwa, abin da ya jawo ya aikata laifin kenan, kamar yadda rahoton hukumar ya nuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel