Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Zamfara, Sun Halaka Masu Azumi da Dama

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Zamfara, Sun Halaka Masu Azumi da Dama

  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai mummunan farmaki a kauyen Ɓaure da ke Zamfara, sun halaka masu azumi da dama
  • Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya sanar da cewa maharan sun farmaki garin a kan babura akalla 30
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar, da mai magana da yawun gwamnan jihar ba su ce komai a kan harin ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Zamfara - Al'ummar garin Ɓaure da ke ƙaramar hukumar Gusau, jihar Zamfara, sun shiga tashin hankali bayan da wasu 'yan bindiga suka kai masu hari.

Yan bindiga sun kai hari kauyen Zamfara
Zamfara: Mahara sun kai farmakin lokacin da al'umma ke shirin buda baki. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

'Yan bindigar sun kai farmakin ne da yammacin ranar Talata, lokacin da al'ummar garin ke shirin buɗa baki, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe manoma da dama, sun tafka mummunar ɓarna ana azumi a jihar Arewa

Sunayen mutanen da aka kashe a Zamfara

Wani mazauna garin, da ya zanta da BBC Hausa, ya bayyana cewa maharan sun bude wuta kan mai uwa da wani a lokacin da suka dura cikin garin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce 'yan bindigar sun kashe mutane biyu tare da jikkata wasu, daga bisani mazauna garin da ke makwabtaka da su suka kawo masu dauki.

"Sun kashe mana Aliyu Abubakar na gidan Zuma da Musa Barkono na hayin Suto, yayin da aka kwantar da mutane biyar a asibiti.
"Sun shigo mana garin saman babura akalla 30, kowannensu yana dauke da mugayen makamai, hankalin mu ya tashi sosai."

- A cewar mazaunin garin.

"'Yan bindiga sun yi kwantan ɓauna" - Mazauni

Wani mazaunin garin shi ma ya labarta yadda aka kai masu farmakin yana mai cewa:

"Sun fara zuwa a babura biyu, suka ce mu ba su kayan tallafin da aka bamu, sai muka kore su, ashe sun yi mana kwantan ɓauna ne.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan mutumin da ya sace Alkur'anai a Masallaci, ta ba shi zaɓi 1 a Abuja

"Jim kadan sai muka ga sun dawo tare da 'yan uwansu akan babura 30 kowanne dauke da bindiga, suka bude wuta har suka kashe mutum biyu."

Mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris da kakakin rundunar 'yan sandan jihar ba su ce uffan a kan harin ba.

An kashe shugaban 'yan bindiga a Zamfara

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa rundunar sojin sama ta yi luguden wuta kan 'yan bindiga da suka yi yunkurin kai hari wani kauyen Zamfara.

Rahoto ya nuna cewa cikin wadanda aka kashe a farmakin, akwai Kachallah Damina, shugaban 'yan bindiga da ya addabi Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel