Atiku Abubakar Ya Maida Zazzafan Martani Kan Garkuwa da Ɗalibai da Ƴan Gudun Hijira a Jihohi 2

Atiku Abubakar Ya Maida Zazzafan Martani Kan Garkuwa da Ɗalibai da Ƴan Gudun Hijira a Jihohi 2

  • Alhaji Atiku Abubakar ya mayar da martani kan garkuwa da ƴan gudun hijira, malamai da ɗalibai a jihohin Borno da Kaduna
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya nuna damuwa kan yadda gwamnatin APC ta gaza samar da abu mafi muhimmanci ga ƴan ƙasa
  • Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro su farka daga bacci, su ceto mutane masu raunin da aka yi garkuwa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa a zaben 2023 a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan sace ƴan gudun hijira, malamai da ɗalibai a jihohin Kaduna da Borno.

Atiku ya yi martani kan hare-haren garkuwa da mutane ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X ranar Jumu'a, 8 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane matsorata ne, sun cancanci hukuncin kisa, Remi Tinubu ta magantu a bidiyo

Atiku Abubakar.
Atiku Abubakar Ya Yi Martani Kan Garkuwa da Ƴan Gudun Hijira da Dalibai a Kaduna da Borno Hoto: @Atiku
Asali: Getty Images

Kimanin dalibai 287 ne suka bace bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a makarantar gwamnati da ke Kuriga, karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A Borno, sama da 'yan gudun hijira 200 ne 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su daga sansaninsu da ke karamar hukumar Ngala ta Borno ranar Talata.

Atiku ya yi magana kan waɗannan hare-hare 2

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce rashin tsaro a kasar nan na kara ta'azzara da muni a kowace rana.

Ya zargi gwamnatin jam’iyyar All Progressives Congress da gazawa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma.

Atiku ya ce:

“Kafofin yada labarai sun cika da rahotannin ƴan bindiga, garkuwa da mutane, da zubar da jini wanda ya mayar da kasarmu wata kila daya daga cikin yankunan da aka fi fama da ta’addanci a duniya.

Kara karanta wannan

Dan Ganduje ya samu muƙami da Tinubu ya dakatar da Shugaban REA a kan N2bn

"A cikin mako guda, an sami rahotanni da dama na yin garkuwa da mutane marasa galihu a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin kasar nan.
"Abubuwan ba su da iyaka, gwamnatin APC ta gaza mafi munin gazawa wajen samar wa mutane abu mafi muhimminci da suke sa ran samu daga gwamnati mai tausayi."

Atiku ya aike da saƙo ga Tinubu da hukumomin tsaro

Alhaji Atiku ya kuma caccaki gwamnati mai ci kan sauye-sauyen da take ikirarin tana yi na gyara a daidai lokacin da masu rauni ke cikin wahala.

"Wannan ya saba wa nauyin da tsarin mulki ya ɗora kan gwamnati cewa tsaro da jin dadin ‘yan kasa su ne manyan abubuwa da suka rataya a wuyan gwamnati.”
"Ina tare da ’yan uwana ƴan Najeriya da kuma jajantawa wadanda abin ya shafa da iyalansu."

- Atiku Abubakar.

Atiku ya bukaci hukumomin tsaro da su tashi tsaye wajen ganin sun ceto ‘yan kasar da ba su ji ba ba su gani ba daga hannun ‘yan bindiga da ƴan ta'adda.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ruwan wuta a sansanin ƴan bindiga a jihohin Arewa, sun kashe da yawa

Yan bindiga sun kuma kai hari

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun halaka mutane da dama ciki har da ƙaramin yaro a yankin karamar hukumar Gwer ta jihar Benuwai.

Rahoto daga mazauna yankin ya nuna cewa maharan sun ƙona gidaje da yawa yayin harin da suka kai ranar Alhamis da daddare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel