Dalibai Mata Na Jami’ar Gasau da Aka Sace Sun Shaki Iskar ’Yanci Bayan Shafe Tsawon Lokaci a Tsare

Dalibai Mata Na Jami’ar Gasau da Aka Sace Sun Shaki Iskar ’Yanci Bayan Shafe Tsawon Lokaci a Tsare

  • An bayyana sako wasu adadi na daliban da aka sace a jami'ar Gusau da ke jihar Zamfara a Arewacin Najeriya
  • Bayanai sun bayyana yadda aka kai ruwa rana na tsawon watanni tara kafin samun damar sakin daliban
  • Jihohin Arewacin Najeriya na yawan fuskantar sace-sace daga tsagerun 'yan ta'adda masu yawo da makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Zamfara - A ranar Juma'a ne 'yan ta'adda suka sako dalibai mata tara cikin 21 na jami'ar tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara bayan shafe tsawon lokaci a tsare.

Daya daga cikin wadanda suka tsakani aka sako dalibai ya shaidawa jaridar Premium Times cewa, an sako daliban ne bayan shafe akalla watanni tara ana kai-komo kan sakin nasu.

Kara karanta wannan

Dakatar da Sanata Ningi ya haifawa majalisar dattawa fushin kungiyoyin Arewa

Akalla, daliban sun shafe kwanaki 178 a maboyar tsageru tun bayan da aka sace su a watan Satumban baran.

Yadda aka sako sauran daliban Zamfara da aka sace
An sako daliban Zamfara da aka sace | Hoto: @DaudaLawalD
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka sace daliban a watan Satumba

A cewar rahotanni, an sace daliban ne a lokacin da tsagerun suka kai farmaki dakin kwanan dlaibai a Sabon Gari, wani yanke da ke cikin jihar Zamfara.

Hakazalika, ba daliban kadai aka sace ba, an sace wasu mazauna yankin da adadinsu ke da yawan gaske.

Bayan sa'o'i kadan, an ruwaito cewa, jami'an tsaro sun kubutar da wasu daga cikin wadanda aka sacen.

Ba kudi 'yan bindigan ke nema ba

A cewar daya daga cikin wadanda suka shiga tsakani aka tattauna sako daliban ga Premium Times, 'yan ta'addan ba kudin fansa suka nema ba.

A kalamansa:

"Mun fara tattaunawa dasu jim kadan bayan da aka sace daliban. Da fari sun ki ba da hadin kai amma da muka matsa, sai suka saurare mu."

Kara karanta wannan

Gaza: Bam ya kashe ‘yanuwa 36 lokacin shirin sahur a dauki azumin Ramadan

A cewarsa, shugaban tsagerun mai suna Ali Kawaje ne ya jagoranci satar, kuma ya bayyana bacin ransa ga yadda gwamnatin tarayya da ta Zamfara suka kame dan uwansa.

Tinubu ya ba da umarnin ceto daliban Zamfara

A wani rahoton, kun ji yadda shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana tashin hankali game da yadda aka sace daliban jami'a a Zamfara.

Ya kuma ba da umarnin a gaggauta ceto dlaiban da aka sace a dakin kwanan dalibai da ke kusa da jami'ar.

Jihar Zamfara na daga jihohin da ke fama da yawaitar sace-sace daga tsagerun 'yan bindiga masu yawo da makami.

Asali: Legit.ng

Online view pixel