Katsina
Dakarun sojoji da haɗin guiwar ƴan sanda sun samu nasarar ceto ƴan bautar ƙasa biyu duk mata daga hannun 'yan bindiga a jihar Katsina ranar Alhamis.
Dikko Umaru Radda ya yi koyi da Malam Nasir El-Rufai wajen yin aiki da matasa, yanzu ya jawo Khalil Nur Khalil mai shekara 30, ya nada a matsayin Mai bada shawara.
Jami'an ƴan sanda tare da haɗin gwiwar jami'an sojoji sun samu nasarar ceto wasu mutum huɗu da miyagun ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Katsina.
Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai munanan hare-hare a ƙauyukan Domawa da Sukola na jihar Katsina inda suka halaka mutum uku da sace wasu da dama.
Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda ya sake jadadda kudurinsa na kin yin sulhu ko kuma kulla wata yarjejeniya da ‘yan ta’adda. Ya ce ko matarsa ce zai hukunta ta.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda, ya ce ko alama ba zai nemi tattauna wa da yan bindigan daji ba, maimakon haka zai yaƙe su da karfin soji sai sun tuba da kansu.
Masu noman kaji a Katsina sun ji dadin ba Muhammad Abu Ibrahim kujerar NADF. Bola Tinubu ya tuna da iyalin abokinsa, tsohon Sanatan Katsina, Abu Ibrahim.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda zai fara biyan limamai da masu unguwanni alawus-alawus domin su taimaka wajen magance matsalar tsaro a jihar.
Hukumar kula da gidajen gyaran hali reshen jihar Katsina ta bayyana cewa wasu Fursunoni biyu da ke dakon shari'a sun gudu daga kurkuku amma an sake kama ɗaya.
Katsina
Samu kari