Yadda Yan Ta'adda Suka Kashe Yansakai 41 A Harin Kwanton Bauna A Dajin Katsina

Yadda Yan Ta'adda Suka Kashe Yansakai 41 A Harin Kwanton Bauna A Dajin Katsina

  • Mazauna wasu kauyuka da ke karamar hukumar Bakori a Jihar Katsina suna zaman makoki sakamakon rasa yan uwansu da dama
  • Hakan ne zuwa ne yayin da wasu yan ta'adda suka kashe a kalla Yansakai 41 tare da raunata 2 yayin wani artabu a dajin Yargoje
  • Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da afkuwar lamarin tana mai cewa Yansakai din sun bi yan ta'addan daji ne da nufin kwato shanu da suka sace

Jihar Katsina - Wani artabu da aka yi tsakanin yan ta'adda da kungiyar tsaro ta yan sa kai da aka haramta ayyukansu ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum 41 a Katsina.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar wa Channels TV hakan cikin sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Mahara Sun Tare Tawagar Gwamna, Sun Nemi Kudi, Basu Samu ba Sun Jefe Shi Tare da Harbin Ababen Hawa

Katsina
Yadda Yan Ta'adda Suka Kashe Yansakai 41 A Harin Kwanton Bauna A Dajin Katsina. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yansakai sun bi sahun yan bindigan ne bayan sun sace shanu

Ya ce yan haramtaciyyar kungiyar ta Yansakai daga kauyuka 11 a karamar hukumar Bakori, sun hadu sun bi sahun yan ta'addan da nufin karbo shanu da suka sace.

Mai magana da yawun yan sandan ya ce mambobin haramtaciyar kungiyar sun bi sahun yan ta'addan sun gano su a wani wuri a dajin Yargoje inda yan ta'addan suka musu harin kwaton bauna.

Sanarwar ta ce:

"Yan ta'addan sun harbi tare da kashe Yansakai 11 tare da raunta guda biyu. Kwamanda na Malumfashi ya jagoranci tawagar yan sanda zuwa wurin da abin ya faru an kwaso gawarwakin tare da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kankara."

Sanarwar ta kara da cewa:

"Tawagar jami'an tsaro na hadin gwiwa a halin yanzu suna atisaye da nufin gano wadanda suka aikata laifin tare da hukunta su. Ana bincike."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Daba Sun Yi Garkuwa da Ɗan Takarar Gwamnan APC a 2023

Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan yan ta'adda da dama sun kai hari gidan wani Alhaji Muntari a Unguwar Audu gare, yankin Kandarawa a karamar hukumar Bakori inda suka sace shanu 50 da tunkiya 30.

Yan ta'adda sun kai hari tashan jirgin kasa sun sace mutane da dama a Edo

A wani rahoton kun ji cewa wasu yan ta'adda sun sace fasinjoji masu yawa daga tashar jirgin kasa a karamar hukumar Igueben a jihar Edo.

Daily Trust ta rahoto cewa mutanen da aka sace suna shirin shiga jirgin ne don zuwa Warri a lokacin da lamarin ya faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel