Katsina: Yan Majalisar Wakilan Tarayya Uku Sun Fice Daga APC, Sun Koma PDP

Katsina: Yan Majalisar Wakilan Tarayya Uku Sun Fice Daga APC, Sun Koma PDP

  • Jam'iyya mai mulki a jihar Katsina ta ƙara rasa 'yan majalisar tarayya uku yayin da zabe ke kara matsowa
  • Wasu rahotanni sun nuna cewa mambobin majalisar uku sun rasa tikitin APC na komawa majalisar wakilai
  • Hadimin tsohon sakataren gwamnatin Masari, Mustapha Inuwa, yace 'yan majalisun sun gana da Atiku a Sakkwato

Katsina - Mambobin majalisar wakilan tarayya uku daga jihar Katsina sun tattara kayansu daga APC sun koma jam'iyyar PDP bayan sa labule da Atiku Abubakar a Sakkwato ranar Lahadi.

Majiyar Premium Times ta tattaro cewa manyan hadimai 2 na tsohon Sakataren gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa, ne suka kai gwauro suka kai mari suka haɗa ganawa tsakanin yan majalisun da Atiku.

Manyan jam'iyyu a Najeriya.
Katsina: Yan Majalisar Wakilan Tarayya Uku Sun Fice Daga APC, Sun Koma PDP Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

'Yan majalisun uku waɗanda suka bar APC sune, Hamza Dalhatu na mazabar Rimi, Charanci da Batagarawa, Salisu Iro na mazaɓar Katsina da Ahmad Ɗayyabu na mazaɓar Ɗanmusa, Safana da Batsari.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Shiga Sabon Ruɗani, Manyan Jiga-Jigan PDP Da Dubannin Mambobi Sun Koma APC a Arewa

Haka nan wasu manyan 'yan kasuwa guda biyu, Bilyaminu Funtua mai kamfanin NAK Enterprises da Kabir Kabir Bilya, waɗanda suka kasance fitattun mambobin APC sun koma PDP bayan zama da Atiku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa 'yan majalisun uku sun gaza lashe tikitin neman komawa majalisar wakilai ta ƙasa lokacin zaɓen fidda gwanin APC a shekarar bara.

Yadda suka gana da Atiku a Sakkwato

Ɗaya daga cikinn hadiman, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da hurumin zantawa da yan jarida, ya gaya wa Premium Times cewa tun farko 'yan majalisar sun nuna shirinsu na barin APC.

A cewarsa, sun nemi zama da Atiku na PDP kafin yanke shawara ta karshe. Mutumin ya ce:

"Kunsan muna fama da rigimar shugabanci a PDP reshen Katsina. Suna son sauya sheƙa amma ba su da tabbacin yadda za'a karbe su amma Oga (Inuwa) ya shawo kansu."

Kara karanta wannan

2023: Arewa Na Neman Kucce Wa Tinubu, Dan Majalisar Tarayya Ya Fice Daga Jam'iyar APC

"Sun nemi samun tabbacin za'a mutunta su kamar sauran mambobin jam'iyya. Bayan Ralin Charanci nan take ya (Inuwa) tuntubi Atiku kuma aka amince a tafi da su Sakkwato."
"Suna nan tare da mu kuma da su zamu tafi jihar Zamfara yau (Litinin 30 ga watan Janairu) domin halartar ralin shugaban kasa."

Ɗayyabu da Iro ba su sanar da ficewa daga APC ba gabanin wannan ganawa ranar Lajadi amma Ɗalhat ya sanar da batun barin jam'iyya mai mulki a wata wasika da ya tura ga shugaban APC na gundumarsa.

Da aka tuntube yan majalisun ba su daga waya ba amma ɗaya daga cikin Hadiman Honorabul Iro, ya tabbatar da batun kana ya turo Hotunan zamansu da Atiku.

Dalilin da yasa nake goyon bayan Tinubu duk da ina PDP, Sanata Nnamani

A wani labarin kuma Sanata Nnamani daga jihar Enugu ta fallasa abinda PDP ta yi da ya sa ya yanke shawarar marawa Tinubu baya

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyun Siyasa 40 Sun Yanke Shawara, Sun Fadi Wanda Zasu Marawa Baya Tsakanin Atiku da Tinubu

Nnamani, tsohon gwamnan jihar Enugu ya ce PDP ba ta da adalci da daidaito tun da ta mika tikitin shugaban kasa ga ɗan arewa.

Ya kuma bayyana yadda ta faru gabanin zaɓen 2019 a Patakwal da kuma rashin adalcin da ya biyo a baya yanzu kafin zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel