Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Gillar Da Yan Bindiga Suka Yi Wa Yan Sa-Kai a Katsina

Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Gillar Da Yan Bindiga Suka Yi Wa Yan Sa-Kai a Katsina

  • Shugaban kasa Buhari ya yi martani a kan mummunan harin da yan bindiga suka kaiwa yan sa-kai a jiharsa ta Katsina
  • Yan bindiga sun kai harin kwauton bauna kan yan sa-kai a yayin da suka bi sahunsu don kwato shanu da dabbobin da suka sace
  • Da yake mika ta'aziyyarsa ga yan uwan mamatan, Buhari ya ce ba za a taba mantawa da sadaukarwarsu ga garuruwansu ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da mummunan harin da yan bindiga suka kai wa yan sa-kai a dajin Yargoje da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Wasu yan bindiga sun kai harin kautan bauna kan ayarin yan sa-kai a dajein yayin da suka je kwato dabbobin da maharan suka sace, lamarin da ya kai ga kisan, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karancin Mai Da Kudi: An Yi Kare Jini Biri Jini Yayin Zanga-zanga a Wata Jahar Najeriya, An Kashe Mutum Daya

Buhari
Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Gillar Da Yan Bindiga Suka Yi Wa Yan Sa-Kai a Katsina Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Ba za a manta sadaukarwar wadannan jarumai ba, Buhari

Shugaban kasar a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya saki a ranar Lahadi, 5 ga watan Fabrairu, ya yi ta'aziyya ga dukkanin yan sa-kai da yan uwan wadanda suka mutu a harin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaba Buhari ya ce ba za a taba mantawa da sadaukarwar jaruman mazan ba wadanda ke aiki ba ji ba gani don hana aikata laifuka da hukunta masu yinsa a garuruwansu, rahoton The Nation.

Buhari ya yi wa mamatan addu'a inda ya ce:

"Tunaninmu da addu'o'inmu na tare da yan uwan mamatan a wannan mawuyacin lokaci. Allah ya ji kan wadanda suka rasun."

Harin kwauton bauna: Yan ta'adda sun kashe yan sa-kai a dajin Katsina

A baya mun ji cewa an yi arangama tsakanin yan ta'adda da kungiyar tsaro ta yan sa-kai a jihar Katsina lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla guda 41.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Ta'adda Suka Kashe Yansakai 41 A Harin Kwanton Bauna A Dajin Katsina

Kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar al'amarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a.

Isah ya ce yan sa-kai daga kauyuka 11 a karamar hukumar Bakori, sun hadu sun bi sahun yan maharan da nufin karbo shanu da suka sace. Sun gano su a wani wuri a dajin Yargoje inda yan ta'addan suka musu harin kwaton bauna.

Karancin Naira: Fada ya kaure tsakanin masu zanga-zanga da jami'an yan sanda a Ibadan

A wani labari na daban, mun ji cewa rikici ya kaure yayin da mazauna a jihar Oyo suka gudanar da zanga-zanga kan karancin Naira da man fetur.

An yi arangama tsakanin jami'an tsaro da wasu yan daba lamarin da ya yi sanadiyar rasa ran wani mutum daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng