Tinubu Ya Ba Ahalin ’Yan Sai da Aka Kashe a Katsina Kyautar N100m, Ya Mika Sakon Ta’aziyya

Tinubu Ya Ba Ahalin ’Yan Sai da Aka Kashe a Katsina Kyautar N100m, Ya Mika Sakon Ta’aziyya

  • Dan takarar shugaban kasa a APC ya bayyana jimami da rashin jin dadi kan yadda wasu ‘yan ta’adda suka kashe ‘yan sa kai a Katsina
  • Bola Tinubu ya ba da tallafin N100m ga ahalin wadanda aka kashe tare da mika sakon ta’aziyya garesu da gwamnatin jihar
  • Idan baku manta ba, wasu ‘yan ta’adda sun hallaka ‘yan sa kai a wani kazamin harin da suka kai wani yankin jihar Katsina

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya ba da tallafin N100m ga ahalin ‘yan sa kai da wasu ‘yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da APC ta yi shawarin soke taron gangami da tallata ‘yan takara da ta shirya yi a jihar ta Katsina a jiya Litinin 6 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Masu Tunanin Akwai Wani Sabani Tsakanina da Buhari Za Su Ji Kunya Inji Tinubu

Batun ba da tallafin ya fito ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Buhari ya fitar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tinubu ya tallafawa ahalin wadanda aka kashe a Katsina
Tinubu Ya Ba Ahalin ’Yan Sai da Aka Kashe a Katsina Kyautar N100m, Ya Mika Sakon Ta’aziyya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari ya mika godiyarsa ga tsohon gwamnan na Legas, Tinubu bisa tallafawa ahalin wadanda abin ya shafa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta’aziyyar Tinubu ga ‘yan Katsina

Da yake mika ta’aziyyarsa da jimami ga Buhari da Masari, Tinubu ya ce:

“Jiya mun tattauna kan kodai mu ci gaba da gangaminmu ko mu soke shi. Idan muka soke shi, zai nuna sun yi nasarar cimma abin da suke so.
“Babu abin da zai faru a rayuwa sai da sanin Allah madaukaki. Za mu ci gaba da kamfen dinmu, kuma mu share masheka.
“Sun aikata mummunan laifi a idon ubangiji da kuma duniya. Babu addini ko al’ummar da za ta halasta jinin wadanda basu ji ba basu gani ba.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

“Mun ji zafi da radadin rashin da aka yi. Allah ne kadai zai iya kawar da radadin matan da aka kashe mazajensu da sauran masoyansu.
“Mashekan basu yi nasara ba, ba kuma za su taba nasara ba. Mugunta za ta kau. Za mu kawar da masu tada rikici a Najeriya.”

Tinubu ya kuma bayyana cewa, Buhari makiyin tashin hankali da rashin adalci ne, kuma ba zai aminta da ayyukan ta’addanci ba, Arise Tv ta ruwaito.

A tun farko, rahotonmu ya bayyana yadda ‘yan ta’adda suka kai hari kan ‘yan sa kai a Bakori ta jihar Katsina, sun hallaka mutum 31.

Asali: Legit.ng

Online view pixel