Kungiyar CAN Ta Yi Wa Masari Wani Karamci Da Bata Taɓa Yi Wa Kowa Ba A Tarihi Tun Kafuwarta

Kungiyar CAN Ta Yi Wa Masari Wani Karamci Da Bata Taɓa Yi Wa Kowa Ba A Tarihi Tun Kafuwarta

  • Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya samu lambar yabo na 'Abokin Coci' daga kungiyar CAN ta jihar Katsina
  • Rabaran Fada Richard Shuaibu-Liti, shugaban CAN na Katsina ya ce wannan shine karo na farko da aka bada irin wannan lambar yabon a tarihin kungiyar
  • Shuaibu-Liti ya ce sun karrama Masari ne saboda hidimdimu da ya rika yi wa kiristoci da janyo su a jiki a jihar cikin shekaru bakwai na mulkinsa ciki har da daukan nauyin mutum 300 zuwa kasar Isra'ila da nada mambobinsu mukami a gwamnatinsa

Katsina - Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, ta karrama gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da lambar yabo na Abokin Coci saboda ayyukan alheri da ya yi wa sashin CAN na jihar, rahton This Day.

Gwamnan ya samu irin wannan lambar yabon, karo na farko a kasar, a ranar Asabar bayan taron addu'a na kwana biyu da CAN ta shirya, wanda aka yi a cocin Anglican, GRA, Katsina.

Kara karanta wannan

Wani Ya Shiga Katuwar Matsala a kan Zargin ‘Danuwan Buhari da Ganin Bayan Tinubu

Masari da CAN
Kungiyar CAN Ta Yi Wa Masari Wani Karamci Da Bata Taɓa Yi Wa Kowa Ba A Tarihi Tun Kafuwarta. Hoto: This Day
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban CAN na jihar, Rabaran Fada Richard Shuaibu-Liti, yayin mika lambar yabon, ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen gwamna wanda ya nuna halaye nagari a shugabancinsa tare da tafiya tare da kowa.

Ya ce:

"Mu a matsayinmu na shugabanin kiristoci a Katsina muna son nuna godiyarmu ga Gwamnan Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, wanda ba wai kawai ya nuna kyakkyawan salon shugabanci ba, amma ya yi jagoranci da ya hada da kowa kuma muna son bashi lambar yabo ta 'Abokin Coci'. Wannan lambar yabon ita ce irinta na farko a tarihin kungiyar.
"Babban dalilin da yasa shugabannin CAN na jihar dukansu suka amince a karrama mai girma abu ne mai sauki, kai ne gwamna a Katsina na farko wanda ya jawo coci a jiki har ka nada wasu mambobinmu a matsayin SSS (babban mataimaki na musamman) kan harkokin kirista, SA (babban mataimaki) kan harkokin mata kirista da SA kan yan asalin Najeriya a gwamnatin ka."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Na San Yadda Zan Yadda Zan Gyara Tattalin Arzikin Najeriya, Bola Tinubu

Ya yi bayanin cewa gwamnan ya kashe biliyoyin naira don daukan nauyin fiye da kiristoci 300 zuwa ziyarar kasa mai tsarki na Isra'ila a shekaru bakwai da suka wuce na mulkin ka a sassan jihar.

Amma, shugaban na CAN ya roki Gwamna Masari ya saka koyar da darasin addinin kirista (CRK) a tsarin koyar da makarantu na jihar don a fara koyar da darasin a makarantun gwamnati da na kudi kafin karewar wa'adinsa na biyu.

Martanin Gwamna Masari

A bangarensa, Gwamna Masari ya ce kiristan da ke jihar ba mazauna bane amma yan jiha, ya shawarci su dena zuwa wasu jihohin don samun takardar yan jiha amma 'su tsaya a nan su kwaci hakkinsu.'

Ya ce rashin shugabanci na gari da ilimi na ya janyo matsalolin da ke damun kasar, ya yi kira ga iyaye kirista su rika saka yayansu a makaranta.

A jawabinsa, SSA ga Gwamna Masari kan harkokin kirista, Rabaran Ishaya Jurau ya ce gwamnatin Masari ne kadai a arewa maso yamma ta ke daukan nauyin kiristoci zuwa kasar mai tsarki kuma shine gwamna na farko wanda ke 'kwance' da coci a arewa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Goyi Bayan Buhari, Ya Fallasa Manufar Canja Kuɗi Ana Gab da Zaben 2023

Masari ya zubar da hawaye yayin gabatar da kasafin kudinsa na karshe

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnan jihar Katsina ya zubar da hawaye yayin gabatar da kasafin kudin gwamnatinsa na karshe ga majilisar dokokin jiha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel