Ina da Tabbacin Tinubu da Sauran Ƴan Takarkarun APC ne Zasuyi Nasara Tun a Zagayen Farko

Ina da Tabbacin Tinubu da Sauran Ƴan Takarkarun APC ne Zasuyi Nasara Tun a Zagayen Farko

  • Buhari ya bayyana Kwarin Guiwar sa Kan APC zata Lashe Zaɓuka Kwaf-Daya Jim Kadan da Kada Ƙuriar sa A ranar Asabar Ɗin Data Gabata.
  • Buhari ya Hori Ƴan Takarkarun dake Kowacce Jam'iyya Dasu Amshi Sakamakon Zaɓen da Za'a Sanar, Yace Dole Mutum Ɗaya Zai Nasara.
  • Yayi wa Ƴan Najeriya Alƙawarin Barin Tarihin Yin Zaɓe Mafi Kyau da Sahihanci a Tarihin Najeri

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna ƙwarin guiwar sa akan ilahirin ƴan Takarkarun da jam'iyyar APC ta tsayar dake fafatawa a zaɓen 25 ga watan Fabrairu na 2023.

Ya da bada tabbacin cewa ƴan takarkarun APC ne zasuyi Nasara a zaɓukan da za'a gudanar 25 ga Fabrairu da kuma wanda za'a gudanar na 11 ga watan Mayu.

Shugaban ya sanar da hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ya jefa ƙuriar sa a akwatin sa na 003, Sarkin Yara A, a can Daura dake Jihar Katsina a ranar asabar din data gabata.

Kara karanta wannan

Yadda Masu Kada Kuri'a Sukayi Karanci Basu Fito ba a Kaduna Ya Dame Ni - El-Rufai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari
Ina da Tabbacin Tinubu da Sauran Ƴan Takarkarun APC ne Zasuyi Nasara Tun a Zagayen Farko- Muhammdu Buhari Hoto: Legit.ng
Asali: Depositphotos

Shugaban ƙasar daya zanta da manema labaran da harshen turanci da Hausa ya shaida cewa:

"Ina matuƙar farin ciki akan yadda aka bi tsarin gudanar da zaɓen nan. Musamman ma akan yadda masu kaɗa kuri'a suka fito ƙwansu da ƙwarƙwatar su, yayi matuƙar ƙayatar dani.
"Duk ƴan takarkarun mu na APC daga Daura zuwa Legas zasuyi nasara ba shakka. Musamman ma a zaɓen yau da ake gudanar (Asabar) da kuma na 11 ga watan Mayu." Inji shi.

Buhari ya kuma yi amfani da damar wajen kiran masu kaɗa kuri'a a Adamawa dasu yi farin ɗango su tuttulawa mace ɗaya tilo ƙuriar su a zaɓen gwamnan jihar, wato Hajiya Aishat Binani.

Shugaban wanda yazo wajen kaɗa ƙuriar shida matar sa A'isha Buhari da sauran ahali, dukkan su sun kaɗa kuri'un su ne a wannan akwatu.

Kara karanta wannan

Tabbas Ina da Ƙwarin Gwuiwa Cewar Nine Zan Lashe Zaɓen Nan - Tinubu

Shugaba Buhari da iyalin sa sun isa wajen ne da misalin ƙarfe 9:57 na safe yayin da mutane keta musu shewa cike da shauƙi.

An tantance shi jim kaɗan bayan isarsa wajen, inda ya ɗimfari wajen akwatun sa ya kaɗa kuri'a.

Shima Shugaban, baiyi wata wata ba ya maida martani na gaisuwa da jinjina ga mutanen dake ta faman shiga shauƙi da kuma murnar ganin sa.

Daga karshe ya hori duk yan takarkaru da su amshi sakamakon zaɓen da akeyi da zuciya ɗaya, inda ya jaddada cewa, dole mutum ɗaya ne a ko wanne irin zaɓe zaiyi nasara, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Duk a batun zaɓen dai, INEC tayi barazanar soke zaɓukan jihar Kogi.

Me Yasa INEC Ke Barazanar Soke Zaɓukan Jihar Kogi?

Kwamishinan Zaɓe na jihar Kogi shine ya tura saƙon yiwuwar hakan lokacin da yake maida martani abisa rigimar data ɓarke a wasu ƙananan hukumomi na jihar.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Yayi Allah Wadai Da Kisan Ɗan Takara Ana Dab Da Zaɓe, Ya Ba Jami'an Tsaro Wani Umurni

Legit Hausa ta ruwaito cewar an samu rahotannin ne na wasu yan jagaliyar siyasa da suka shiga guraren akwatunan zaɓe a Anyigba da Dekina dake gabashin Kogi suka aikata ta'annatin da har yakai ga wannan tunani daga INEC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel