Yan Sanda Sun Kama Mutum 15 Da Kwamfutoci Don Yin Kutse a Sakamkon Zabe

Yan Sanda Sun Kama Mutum 15 Da Kwamfutoci Don Yin Kutse a Sakamkon Zabe

  • Rahotanni da ke zuwa sun tabbatar da cewar an kama mutumn 15 a jihar Katsina a jajiberin zaben 2023
  • A cewar rundunar yan sandan jihar, ana zargi su dukka mutanen 15 suna shirin kawo tsaiko ga sakamakon zaben
  • An kama wadanda ake zargin dauke da kwamfutocin laftofkuma shirin amfani da su wajen yin kutse a sakamakon zabe

Katsina - Rundunar yan sandan jihar Katsina ta ce ta kama wasu mutane 15 kan zargin shirin yin kutse a sakamakon zabe yayin da aka fara babban zaben kasar.

Kakakin rundunar yan sandan jihar SP Gambo Isah, wanda ya tabbatar da kamun shine ya sanar da ci gaban a daren ranar Juma'a, 24 ga watan Fabrairu.

Jami'an yan sanda
Yan Sanda Sun Kama Mutum 15 Da Kwamfutoci Don Yin Kutse a Sakamkon Zabe Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cewar Isah, an kama wadanda ake zargin ne kan kasancewa dauke da kwamfutocida manhaja da ake zargin mallakin wani shahararren dan siyasa ne a jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Saura Yan Awanni Zabe, Jam'iyyar APC Ta Dakatar Da Sanata Orji Uzor Kalu

Yan sanda na gudanar da bincike, SP Gambo Isah

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, an tsare wadanda ake zargin a sashin binciken masu laifi don ci gaba da bincike.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar Thisday ta nakalto Isah yana cewa:

"Mun kama mutane goma sha biyar da wasu adadi na kwamfutocin laftof da wasu manhaja mallakin wata jam'iyyar siyasa.
"Mun fara gudanar da bincike kuma ba ma so mu yanke hukunci kai tsaye. Mun rigada mun gayyaci kwararru don gudanar da bincike kan kayayyakin don bama son yanke hukunci kai tsaye. Za mu sanar da sakamakon binciken."

Sai dai kuma, an shawarci mazauna Katsina da su zauna lafiya yayin gudanar da zaben.

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa an tura jami'ai zuwa wurare masu miuhimmanci don hana kawo hari.

Ya bayyana cewa an bayar da umurnin takaita zirga-zirgar mutane da ababen hawa a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hoto, Bayanai Sun Fito Yayin Da Yan Sanda Suka Kama Sanannen Dan Majalisar Wakilai Da Dala 498,000 Cikin Jaka

Yadda babban zaben shugaban kasa ke gudana a fadin Najeriya

A gefe guda, Legit.ng na ta dauko rahoto kai tsaye kan yadda babban zaben shugaban kasa ke gudana a yau Asabar, 25 ga watan Fabrairu a fadin Najeriya.

Ana fafatawa tsakanin Atiku Abubakar dan takarar jam'iyyar PDP, Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar APC, Peter Obi na jam'iyyar Labour Party da kuma Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel