Tun Ana Yara Na San Shi: Buhari Ya Yi Jimamin Rashin Dattijon da Suka Taso Tare

Tun Ana Yara Na San Shi: Buhari Ya Yi Jimamin Rashin Dattijon da Suka Taso Tare

  • Mai girma Muhammadu Buhari ya fitar da sakon ta’aziyya na mutuwar Sanata Abba Ali a jiya
  • Shugaban Najeriyan ya ce ya yi rashin aboki mai daraja bayan samun labarin cikawar Abba Ali
  • Dattijon ya yi sakandare tare da Buhari, har ya bar Duniya akwai kyakkyyawar alaka tsakaninsu

Katsina - Shugaba Muhammadu Buhari ya na jimamin mutuwar tsohon Sanatan Najeriya, Abba Ali, wanda ya kasance tsohon abokinsa a rayuwa.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa Abba Ali ya cika ne a ranar Talata, 14 ga watan Fubrairun 2023, kuma tuni har an birne shi a kasar Saudi Arabiya.

Majiyarmu ta ce Sanata Abba Ali bar Duniya ne bayan jinyar rashin lafiya na wani gajeren lokaci a asibitin Saudiyya, inda a nan aka yi jana'izarsa.

Premium Times ta rahoto Muhammadu Buhari ya yi magana a kan rasuwar wannan Bawan Allah wanda ya ce cikakken dattijo ne da ya fahimci kasa.

Kara karanta wannan

Buhari Bai Yi Kokari Sosai a Nan ba, Jigon APC Ya Fadi Bangare 1 da Tinubu Zai Gyara

Nayi rashin aboki mai daraja

Shugaban Najeriyan ya ce ya samu damar sanin Marigayin tun su na tasowa, ya ce yanzu ya bar su a Duniya, yake cewa za suyi matukar kewansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sakon ta’aziyyar Mai girma Muhammadu Buhari ya fito ne ta bakin Mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu da yammacin ranar Talata a Abuja.

Buhari
Shugaba Buhari a Fadar Sarkin Katsina Hoto: @GarShehu
Asali: Twitter

Garba Shehu ya yi wa ta’aziyyar shugaban kasar take da “Na rasa aboki mai daraja.”

Abba Ali ya rike mukamai

Abba Ali ya rike kujerar shugaban kungiyar daliban makarantar gwamnatin Katsina watau GCK, inda Shugaba Buhari da wasu dalibai suka halarta.

PM news ta fitar da rahoto cewa Marigayi Abba Ali ya na cikin shugaban majalisar da ke sa ido a kan harkar aikin ma’aikatan shari’a a kasar nan.

Kara karanta wannan

Sarkin Ibo Ya Yi wa Shugaban Kasa Abin da ba Zai Manta ba Har ya Bar Duniya

Abba Ali ya taba Sanatan Katsina kafin Janar Muhammadu Buhari ya hambarar da gwamnati.

Allah ya jikan Abba Ali

Buhari Sallau wanda yana cikin masu ba shugaban kasa shawara ya yi wa mamacin addu’a a shafinsa na Facebook bayan samun labarin, yace:

Allah Ya gafartawa Sanata ABBA ALI, Yasa Aljannatul Firdausi Makoma. Ameen Ya Allah.

Yadda abin ya faru

Hafiz Yakubu Stores ya shaidawa Legit.ng Hausa cewa a ranar 31 ga watan Junairu 2023, tsautsayi ya jawo wata ta buge Abba Ali a mota a Saudi.

A lokacin da wannan hadari ya auku, Sanata Ali yana rike da Kur'ani a hannunsa.

A cewar wannan matashi, tun lokacin Marigayin yake jinya a asibiti, bayan makonni biyu ya rasu. Abba Ali ya je Saudiyya ne domin yin aikin Umrah.

Farfesa Pate zai shugabanci Gavi

An ji labari Farfesa Muhammad Ali Pate wanda ya yi Ministan lafiya a Gwamnatin Jonathan ya samu daukaka, zai rike Gavi da ke Switzerland.

Kara karanta wannan

Dalilin Canza Kudi, Mai Martaba Ya Koka da CBN, Babu N20, 000 a Cikin Fadar Sarki

Shugaba Umaru ‘Yaradua ya fara dauko Muhammad Ali Pate, ya ba shi shugabancin Hukumar NPHCDA a 2008 kafin ya zama Ministan kiwon lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel