Zaben 2023: An Cafke Mutum 15 A Katsina Kan Zargin Canja Alkalluman Zabe

Zaben 2023: An Cafke Mutum 15 A Katsina Kan Zargin Canja Alkalluman Zabe

  • Rundunar yan sandan Jihar Katsina ta kama mutane 15 bisa zargin yunkurin chanja alkaluman zabe
  • Hukumar ta cafke mutanen da yammacin Juma'a dauke da kamfutoci kanana da ba a san adadin su ba
  • Zabe ya gudana lafiya da safiyar Asabar a fadin jihar yayin da jami'an suka girke jami'an ta a wurare da dama

Jihar Katsina - Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Katsina sun yi nasarar kama mutane 15 a jihar ranar Juma'a bisa zargin shirin canja alkaluman zabe.

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da kama mutane da daren Juma'a, rahoton The Punch.

Katsina Map
Taswirar Jihar Katsina. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Ya ce an kama mutanen a Katsina da kamfutoci da ba a bayyana adadin su ba da ake zargin na jam'iyya daya ne.

Ya ce sun tsare mutanen a sashen lura da manyan laifuka CID na hukumar, yana mai cewa tuni sun yi nisa a bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sace na'urar aikin zabe a jihar su Buhari da kuma wata jihar

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

''Mun kama mutane 15 dauke da kananan kamfutoci da ba san adadin su ba dauke da manhajar wata jam'iyya. Mun fara bincike kuma ba ma son wuce gona da iri.
"Mun gayyaci kwararru don binkice kan kayyayakin saboda bama son gaggawa. Za mu sanar da al'umma halin da ake ciki game da binciken.''

A daya bangaren, Katsina na cikin amincin a safiyar Asabar saboda irin matakan da jami'an tsaro suka dauka a wurare muhimmai da za a kada kuri'a a fadin jihar.

Ba a hana zirga-zirgar ababen hawa da mutane ba a fadin jihar.

An kuma girki jami'an tsaro a duk hanyoyin shige da ficen Jihar.

Jami'an tsaro sun kama wani mutum dauke da miliyoyin naira na sabbi da tsaffin kudi zai kai wa dan siyasa a Gombe

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Ta'adda Sun Kai Hari Rumfar Zabe, Sun Banka Wa Akwatin Zabe Wuta

A wani rahoton kun ji cewa hukumar yaki da rashawa na ICPC ta kama wani Hassan Ahmed da makuden takardun naira da suka hada da sabbi da tsaffi a yayin da al'umma ke fama da karancin kudi.

Sojoji na 33 Artillery Brigade da ke aikin sintiri a Alkaleri Bauchi ne suka damke mutumin da kudaden cikin jaka ta 'Ghana must go' sannan suka kai shi wurin ICPC.

Ya amsa cewa an bashi kudin ne domin ya kai wa wani dan siyasa a Gombe daga jihar ta Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel