Jihar Imo
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Ebere Udeagu, ya rasu a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba, bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya. Shekarunsa 79.
Hukumar jami’ar jihar Imo a ranar Litinin ta janye daga yajin aikin wata 7 da Kungiyar Malamai na jami’o’in Najeriya suka fada tare da sanar da bude jami’ar.
Kakakin majalisa dokokin jihar Imo, ɗaga daga cikin jihohin kudu maso gabashin Najeriya da APC ke mulki, Kennedy Ibe, ya sauka daga mukaminsa, an nada sabo.
Yan bindigan da suka sace wani mai martaba sarkin Isiala Umudi da ke jihar Imo, Eze Joel Ndenkwo, sun kira, sun nemi a biya naira miliyan 200 kafin su sako shi.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya bayyana ‘yan ta’addan Boko Haram a matsayin ‘yan damfarada zamba da gwamnatinsa ta durkusar tun shekarar 2015.
Shugaba Buhari ya isa jihar Imo domin kaddamar da wasu manyan ayyuka 3.Jirgin samansa ya sauka a filin jiragen sama na Sam Mbakwe karfe 11 na safiyar Talata.
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) a shekarar 2020 a kididdigar kiwon lafiya ta duniya ta nuna cewa adadin rayuwar 'yan Najeriya ya kan kai 62.6 har zuwa mutuwarsu.
Wasu bata gari sun kai hari hedkwatar rundunar yan sandan Najeriya da ke Agwa a karamar hukumar Oguta, Jihar Imo a daren ranar Juma'a sun kashe yan sanda hudu.
Jihar Imo - Mutanen yankin arewacin Najeriya da ke zaune a Jihar Imo, suna cikin fargaba da tashin hankali yayi da wasu 'yan bindiga suka kai musu hari a jihar.
Jihar Imo
Samu kari