'Yan APC Sun Yi Carko-Carko a Jihar Imo Domin Yiwa Tinubu Tarba Mai Kyau

'Yan APC Sun Yi Carko-Carko a Jihar Imo Domin Yiwa Tinubu Tarba Mai Kyau

  • Jiga-jigan APC da mambobinta sun tattara a jihar Imo, inda suka bayyana goyon bayansu ga dan takararsu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu
  • Dan takarar shugaban kas ana APC, Bola Tinubu zai halarci wani taron ‘yan kasuwa a birnin Owerri na jihar
  • ‘Yan siyasa na ci gaba da gangamin kamfen, lamarin da ke kara jawo maganganu da dama a fadin kasar nan

Jihar Imo - Jiga-jigai da ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki sun yi dandazo a ranar Alhamis domin tarbar dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu a birnin Owerri na jihar Imo, The Nation ta ruwaito.

Tinubu zai ziyarci Imo ne domin tattaunawa da wasu jama’a ‘yan kasuwa da suka hada masu zuba hannun jari gabanin babban gangamin kamfen dinsa da za a gudanar a kwanaki kadan masu zuwa.

Kara karanta wannan

2023: An gayyaci Ganduje ya ba da shawari kan yadda za a yi zabe cikin lumana badi

Duk da cewa an takaita mahalarta taron ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu da Tinubu zai tattauna dasu, mambobin APC a jihar sun yi tururuwa domin kawai su ga dan takararsu na shugaban kasa.

Masoyan Tinubu sun taru a Imo, suna jiran ya iso
'Yan APC Sun Yi Carko-Carko a Jihar Imo Domin Yiwa Tinubu Tarba Mai Kyau | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya zuwa lokacin hada wannan an ce Tinubu bai iso Owerri ba, amma an ga taron mabiya APC, ‘yan jarida da mutane da dama da suka jawo cunkoson ababen hawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai je Imo a mako mai zuwa

Duk da cewa shugabannin APC sun yiwa ‘yan a mutum APC bayanin za su gana da Tinubu a mako mai zuwa, duk da haka sai da aka nemo runfunan tarbar wadannan mambobin da suka kagu su ga Tinubu.

The Nation ta ruwaito cewa, mambobin na APC sun taro a harabar inda za a yi taron tun karfe 8:00 na safe, inda suke rawa da waka a hanyar Protea da zagayen inda za a yi taron, Track News tattaro.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Tona Masu Lallaban Shi Wajen Samun Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

Sakataren yada labarai na APC a jihar, Cajethan Duke ya siffanta wannan taro na masoya Tinubu da masoyan asal kuma masu nuna goyon baya ga dan takararsu na shugaban kasa.

A cewarsa:

“Ziyarar da Asiwaju zai kawo ba taron kamfen kamar yadda kuka sani. Za a yi taro ne na jiga-jigan masu masana’antu, masu kamfanoni da ‘yan kasuwa a yankin Kudu maso Gabas da kuma ‘yan takarar jam’iyyar a matakai daban-daban.
“Mambobin da kuke gani na jam’iyyar a nan sun zo ne kawai don nuna goyon baya a aikin kuma ina tabbatar muku basu damu da zafin rana ba matukar akwai Tinubu da APC.”

A makon nan ne jam'iyyar APC ta yi taron gangamin kamfen dinta a jihar Filato, an ga dandazozn masoya da dama, gwamna ya fadi dalilin zaban Jos don bude kamfen APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel