Yajin Aiki: Jami'ar Jihar Imo ta Janye Daga ASUU, Ta Bude Makaranta

Yajin Aiki: Jami'ar Jihar Imo ta Janye Daga ASUU, Ta Bude Makaranta

  • Hukumar jami’ar jihar Imo, IMSU ta yanke hukuncin fita daga Kungiyar ASUU tare da komawa bakin aiki
  • Kamar yadda mai magana da yawun jami’ar ya bayyana, sun yanke wannan hukuncin ne domin gujewa cutar da na baya
  • Ya bayyana cewa akwai dalibai da basu fara karatu ba sannan da masu neman gurbin karatu a halin yanzu

Hukumar jami’ar jihar Imo a ranar Litinin ta janye daga yajin aikin wata bakwai da Kungiyar Malamai masu koyarwa na jami’o’in Najeriya suka fada tare da sanar da cewa zata bude jami’anta domin komawa karatu.

Hukumar ta bayyana hakan ne ga Manama labarai a Oweri ta bakin mai magana da yawun jami’ar Ralph Njoku, Vanguard ta rahoto.

ASUU da FG
Yajin Aiki: Jami'ar Jihar Imo ta Janye Daga ASUU, Ta Bude Makaranta. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Kamar yadda yace, hukumar jami’ar ce ta yanke wannan hukuncin inda tace idan aka cigaba da jini irin za sa dalibai su tafka asara ballantana dalibai da yanzu suka samu gurbin karatu.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa A 2023: Tinubu Na Da Karfin Da Zai Iya Farfado Da Najeriya, Yahaya Bello

Ya ce makaranta bata da matsala da ASUU kuma wannan hukuncin ba zai sa a cutar da na baya ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda yace:

“Hukumar makarantar ta yanke hukuncin bude jami’ar domin cigaba da karatu. Ba mu da wata matsala da ASUU mun bude makaranta domin cigaba da karatu. Malaman da suka shirya zasu iya zuwa su fara karatu.
“Mun yanke wannan hukuncin ne saboda kada mu cutar da na baya. Kamar yadda ba mu fara karatu da wasu ba, wasu suna neman gurbin karatu. Idan mun cigaba da jinkiri hakan zai bata tsarin karatun jami’ar. Don haka muka yanke hukuncin mu yi wa tufkar hanci.”

FG da ASUU: Kotu ta Dage Sauraron Shari'a, Ta Saka Sabuwa Ranar Zama

A wani labari na daban, kotun masana'antu a ranar Litinin ta dage sauararon sharia'a tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i, ASUU, zuwa ranar 16 ga watan Satumba mai zuwa.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Hirar Karshe Da Budurwar Da Dan China Ya Kashe Tayi Da Kawarta, Ya Kasance Akan Mutuwa

Mai shari'a Polycarp Hamman ya dage sauraron shari'ar ne saboda a bai wa gwamnatin tarayya mika dukkan takardun da suka dace don karar, Channels TV ta rahoto.

Gwamnatin tarayya ta garzaya gaban kotun masa'antu ta kasa dake zama a Abuja inda take bukatar a umarci kungiyar malamai masu koyarwa ta jami'o'i, ASUU, da su koma bakin aikinsu a yayin da ake kokarin shawo kan rashin jituwar dake tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel